✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa mutane ke luwaɗi da maɗigo?

’Ya’ya maza suna kishi da iyayensu maza ne da suke jima’i da iyayensu mata.

A kimiyyance, har yanzu babu sahihiyar magana da ta wadatar ga sha’anin masu yin luwaɗi da maɗigo.

Mafi yawan binciken da aka yi ya fi nuni ga halayyarsu ne fiye da abin da ya janyo suke neman jinsinsu.

Akwai nazarce-nazarce da yawa da aka yi a kansu, tun daga zamanin su Sigmund Freud har zuwa yanzu.

A gurin Freud, wanda masanin Mutuntakar dan Adam ne (psychology), masu neman jininsin su sun samo asali ne daga irin yarintar da suka yi.

A gurin Freud, neman jinsi yana farawa ne ta abubuwa biyu: maza masu luwaɗi suna da Oedipus Complex a yayin da mata masu maɗigo suke da Electra Complex.

Ra’ayoyin Freud a kan jima’i na daban ne da ba lallai kan mutane ya dauka ba. Kuma a yanzu kimiyya ta ce ba su tabbata ba.

Amma yana cewa, ’ya’ya maza suna kishi da iyayensu maza ne da suke jima’i da iyayensu mata. To wannan kishin ne yake sawa maza suke neman mata idan sun girma (heterosexuals).

To amma idan suka fahimci iyayensu mazan sun fi karfinsu to sai su saduda su sallama wa maza. To wannan shi ne yake janyo wasu mazan suke neman maza (homosexuals), inji Freud.

A bayaninsa son jima’i da mace yana nuna son da ’ya’ya suke yi wa iyayensu mata ne tun suna yara (Oedipus Complex).

Idan suka fi son iyayensu maza kuma sai su girma su rika yin luwaɗi. Akwai wani ra’i da ake kira Interactionism.

Wannan ra’i yana cewa abubuwa da yawa ne suka hadu suka sa maza ko mata suke neman jinsisu.

Yanayin zamantakewa da yanayin al’adu suna janyowa wasu mazan ko matan su rika neman jinsinsu.

Misali, bincike ya nuna al’ummar da maza ba su fiye ganin mata ba, ko mata ba su fiye ganin maza ba saboda al’adar wariya (sexual segregation) to a nan aka fi samun masu neman jinsi.

Wannan yana faruwa ne saboda mazan da matan suna neman wanda ya kamata su biya bukatarsu da shi ko ita, amma sai su rasa, to wannan sai ya sa su fara neman jinsinsu wajen biyan bukata.

Tarihi ya nuna cewa, a zamanin Abbasiyya lokaci ne da aka fi yin kulle kuma ake ajiye mata a “harem”, inda aka fi yin luwaɗi ko maɗigo a tarihin Musulunci.

Har ta kai karara za ka ga ana bayani da yabo a kan namiji kamar yadda ake yi a kan mata! Sai daga baya malamai suka rika wa’azi sosai da fito da hadisan tsoratarwa a kan neman jinsi sannan aka daina.

To masana Ilimin Zamantakewa na ganin cewa yanayin zamantakewa yana janyo neman jinsi.

Sai dai wani zai tambaya, me ya sa a Turai da ake cakuduwa maza da mata amma kuma an fi neman jinsi?

Wannan kuskure ne. Abin da ya bayyana shi ne kawai a Turai an fi fitowa karara a bayyana ana neman jinsi.

Amma binciken intanet ya nuna cewar mutanen da suke kasashen Larabawa sun fi binciken fim ɗin batsa da yake nuna bayyanai akan maɗigo ko luwaɗi, wanda hakan ke nuna cewa sun fi tunanin yin hakan.

Wani ra’ayi na karshe kuma shi ne na halitta. Wasu masanan suna ganin cewa neman maza yana faruwa ne saboda kwayar halittar da aka haifi mutum da ita.

Saboda haka suke ganin cewa akwai mutanen da suke da abin da ake kira da gay gene.

Wannan ra’ayi za ka ji wasu suna karfafar sa da cewa har a dabbobi a kan samu masu neman jinsinsu, inda hakan ke nuna kwayar halittarsu ce a haka.

Sai dai magana ta gaskiya babu wani cikakken bincike da ya nuna akwai wata kwayar halitta ta “gay”.

Hasashe masu wannan ra’ayi suke yi, amma tun da siyasa ta shiga cikin sha’anin mu’amalar jinsi sai suke karfafar sa kamar wani binciken kimiyya ya tabbatar da hakan.

Dangane da Musulunci kuwa, ijima’in malaman Musulunci sun tafi a kan cewar neman jinsi haramun ne da yake cikin manyan zunubai.

Sai dai kuma ba zunubi ba ne don mutum, mace ko namiji ya ji a ransa yana sha’awar jinsinsa. Laifin sai mutum ya aikata hakan.

Tamkar jin sha’awar zina ne, iya jin ba laifi ba ne, amma aikatawar ita ce laifi.

Hasali ma ga namijin da yake jin sha’awar jinsinsa amma tsoron saba wa Allah ya sa bai aikata ba to lada zai samu na tsoron Allah, kamar yadda hakan ya zo a wani mashahurin hadisi.

Amma abin ki ne kuma mutum ya rika yin duk abin da zai kai shi ga sha’awarar jinsinsa. Daga karshe dai, ga mai wannan tambaya, ina ganin kada ya ji ya tsani ko ya tsangwami wanda ya fada masa cewa yana sha’awar jinsinsa.

Malaman Sufanci na cewa ka tsani laifi ba mai laifi ba. Don haka sai dai ya karfafa masa gwiwar ya ci gaba da kiyayewa kada ya aikata hakan saboda yin hakan babban sabo ne a Musulunci kamar yadda ya zo a littattafan hadisai masu yawa kuma kowa ya sani ana faɗa a wa’azuzzuka.

Allah ne mafi sani.

Aliyu Dahiru Aliyu ne ya rubuta. Za a iya samun sa ta imel: [email protected]