Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ipswich Town, Sam Morsy ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ƙin ɗaura ƙyallen kyaftin mai tallata masu ra’ayin luwaɗi da maɗigo a yayin wasa.
Wani hukunci da Morsy ɗan asalin ƙasar Masar ya yanke na ƙin sanya abin hannun mai nuna goyon baya ga masu yaƙin neman ƙungiyar ’yan luwaɗi da maɗigo ta karɓu a Turai ta hanyar wasanni da ake wa lakabi da “Rainbow Laces” a gasar Firimiyar Ingila ya jawo cece-kuce.
Rainbow Laces dai wani yunƙuri na ganin an tallata harkokin ƙungiyoyin luwaɗi da maɗigo ta samu karɓuwa ta hanyar wasanni wadanɗa ke ƙoƙarin samar da kayayyakin sawa ga ’yan wasa a yayin kakar wasannin ƙwallon ƙafa.
Sai dai Morsy ya yanke hukuncin ƙin amfani da irin waɗannan kayan, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce musamman ga masu ra’ayi irin waɗannan kungiyar da kuma masu sukar lamarin.
A cewar ƙungiyar tasa, Morsy ya yanke hukuncin ɗaura ƙyallen da ya saɓa da wanda ke ɗauke da tambarin ’yan luwaɗi ne yayin da suka sha kashi da ci 1-0 a hannun Nottingham Forest a ranar Asabar saboda dalilai na addini kamar yadda kafar BBC ta rawaito.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa ba wannan ba ne karo na farko da hakan ta faru ba, inda haka ma ya yi yayin wasan Ipswich da Crystal Palace da aka gudanar a daren Talata.
Mutane da dama musamman musulmai da waɗanda ba su goyon bayan ƙungiyoyin luwaɗi sun jinjina wa ɗan wasan inda suka bayyana shi a matsayin gwarzo wanda ya san abin da ya dace.
Sai dai a ɓangaren guda kuma, magoya bayan ƙungiyar ke ganin hakan ya saɓa da dokokin wasannin ƙwallon kafa, na rashin nuna addini ko ƙabilanci a yayin wasa.
Kawo yanzu dai Morsy ya ƙi cewa komai kan lamarin kamar yadda kafar ta BBC ta shaida.
Ba Morsy kaɗai ba, ’yan wasa da dama sun bayyana ƙin amincewarsu da wannan yaƙi na tallata wannan ƙungiya duk da cewa su sukan yi amfani da kayan a lokutan wasa.