✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya kai Shehu Sani ofishin Hisbah na Kano?

Tsohon Sanatan ya kai ziyarar ne don samun karin haske kan aika-aikacen hukumar.

Tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattijai, Shehu Sani a ranar Litinin ya ziyarci hedkwatar hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Da ya ke tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da shugabannin hukumar, Sanata Sani ya ce ya kai ziyarar ne don samun karin haske kan aika-aikacenta.

Ya ce, “An sha fadar abubuwa a kan Hisbah, a matsayina na tsohon Sanata kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, ya na da kyau na ziyarci ofishinsu don na ji daga gare su kan yadda suke gudanar da ayyukansu.

“Na ji dadin yadda suka bayyana min cewar ba za su hana mutane tara gashi irin nawa ba.

“Sannan, sun sanar da ni yadda suke gudanar da ayyukansu musamman abin da ya shafi ta’ammali da giya.

“Sun fada min idan mutum ya yi shigar da ba ta dace ba zai fuskanci hukuncin shari’a,” inji tsohon Sanatan.

Shehu Sani ya kuna jinjina wa hukumar, inda ya ce duk fadin Afirka babu ’yan sandan musulunci da suka kai nagartar na Hisbah.

“A matsayinsu na jami’an tsaro na addini, suna da aiki wajen hada kan jama’a da kuma kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

“Yan ta’adda na amfani da sunan addinin Musulunci suna bata sunan Musulunci da Musulmai.

“Yana da kyau Hisbah su shirya tsari mai kyau da za su fuskanci ’yan bindiga. Akwai bukatar su samar da wasu mutane jarumai da za su kawo karshen ’yan ta’adda a Arewan Najeriya.

“Kazalika akwai bukatar su shiga karkara don wayar wa da mutane kai kan hana su shiga tafiyar ’yan bindiga.

Daga nasa bangaren, Kwamandan hukumar, Harun Ibn Sina, ya bayyana jin dadinsa game da ziyarar tsohon Sanatan.