Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi wa ‘yan kasar a yammacin ranar Litinin da karfe 8:00 na dare ta kafafen yada labarai.
Mista Adesina ya bukaci gidajen rediyo da talabijin a kasar da su dangana da gidan talabijin na kasa, NTA, da kuma babban gidan rediyo na kasa FRCN saboda daukar jawabin.
Kwanaki 14 na dokar hana fita da Shugaba Buhari ya kara a kan wanda ya ayyana tun farko a jihohin Legas, Ogun da Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja saboda hana yaduwar cutar coronavirus zai kare a daren Litinin din.
Za a iya tunawa dai makon da ya gabata gwamnonin jihohi 36 sun bai wa gwamnatin tarayya shawarar janye dokar zaman kulle ta da sanya amma kuma ta tsaurara matakai a kan tarurrukan jama’a.
A wata wasika da gwamnonin suka rubuta a ranar 24 ga watan Afrilu zuwa ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, wanda shi ne shugaban kwamitin da shugaban kasa ya nada saboda yaki da cutar coronavirus, gwamnonin sun kuma ba da shawarar tsaurara dokar saka kyallen rufe fuska.
Wasikar dai ta biyo bayan wani taron da gwamnonin suka yi ne da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu.
Gwamnonin sun kuma bukaci Shugaba Buhari da ya sanya batun hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi; janye dokar hana tafiye-tafiye a kan kayan abinci, kiwon lafiya, man fetur, kayan noma; janye dokar tafiye-tafiye a cikin garuruwa, hana fitar dare, hana tafiye-tafiyen jiragen sama a cikin jawabin da zai gabatar.
Wasikar ta kara da cewa, “A taron da aka yi, kungiyar gwamnonin ta amince ta gabatar da bukatun saboda a shigo da batun cikin jawabin shugaban saboda a samu yanayi na bai-daya a yaki da cutar a matakan jihohi da kuma kasa baki daya”.
A ranar Laraba da ta wuce gwamnonin sun amince da dakatar da tafiye-tafiye tsakanin jihohi na tsawon makwanni biyu saboda iganta yaki da cutar.
A wani jawabi da suka fitar bayan taronsu na shida da suka yi ta yanar gizo, gwamnonin sun zayyana muhimman abubuwa da dokar ba ta shafesu ba.
Kwararru a harkar kiwon lafiya suna ganin kasar na iya bukatar a rufe ko ina saboda yaki da cutar saboda yadda yawan wadanda suka kamu ke karuwa inda a halin yanzu suka haura 1,000.
Aminiya ta gano cewa bukatar gwamnonin ba za ta fara aiki ba har sai wa’adin kwanaki 14 da Shugaba Buhari ya sanya ya kare.
A jiya dai Shugaba Buhari ya karbi bakuncin ministan lafiya na kasar, Dokta Osagie Ehanire da kuma shugaban Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) Dokta Chikwe Ihekweazu.
Taron da suka yi a fadar shugaban kasar, an yi shi ne ba tare da halartar manema labarai ba.
Shugaba Buhari dai yana yi wa ‘yan kasar jawabi ne bayan ya karbi jawabai daga kwamitin yaki da cutar ta coronavirus wanda mutanen biyu suke ciki a matsayin mambobi.
Yayin da yake yi wa ‘yan jaridu bayani bayan ya fito daga ganawa da shugaban kasar, Dokta Ehanire ya ce sun je fadar shugaban kasar ne saboda yi masa bayanin halin da ake ciki da kuma mika masa shawarwari a kan abubuwan da ya kamata a yi.
“Mun kawo cikakken bayani a kan matsayin kwamitinmu wanda ke dauke da minsitoci daban-daban. Mun tattara ra’ayoyin da muke da su kuma mun auna su da yanayin kiwon lafiya, zamantakewa da kuma tattalin arziki muka zo mu gabatar wa shugaban kasa”.
Ministan yace kasar tana samun nasara akan yaki da cutar kuma hakan ya samu ne bayan hukumomin lafiya sun amince su yi aiki tare saboda a gudu tare a tsira tare.
Da yake magana akan yawaitar mace-mace a jihar Kano, Dokta Ehanire ya ce ma’aikatar lafiya ta kasa tana aiki tare da hukumomi daban-daban har ma da gwamnatin jihar ta Kano saboda shawo kan al’amarin.