✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me rahoton ya ce?

  A ranar Talata ce Kwamintin Binciken Sirri na Majalisar Dokokin Amurka ya fitar da rahoton binciken tsige Trump saboda badakalar Ukraine. Kwamitin ya ce…

 

A ranar Talata ce Kwamintin Binciken Sirri na Majalisar Dokokin Amurka ya fitar da rahoton binciken tsige Trump saboda badakalar Ukraine.

Kwamitin ya ce rahoton ya “bankado kokarin da Shugaba Trump ya shafe watanni yana yi na yi wa tsaron kasarmu zagon kasa domin biyan bukatun wasu bincike biyu da ake gudanarwa don cimma manufar siyasa, da za ta taimaka masa a yakin neman sake zabensa.

“Shugaban ya kuma bukaci zababben Shugaban Kasar Ukraine, Bolodymyr Zelensky, ya sanar a bainar jama’a cewa suna gudanar da bincike a kan Joe Biden, wanda shi ne babban abokin hamayyar da Trump din ya fi shakka a zaben da ke tafe.

Trump ya nemi Zelensky ya wofintar da maganganun da ake yi cewa Ukraine ce, ba Rasha ba ta yi katsalanda a zaben Shugaban Amurka a 2016.

Rahoton ya ce ya samu kwararan hujjoji fiye da kima cewa Trump ya saba ka’idar aikinsa kuma ya kawo wa majalisar kasar tarnaki. Kamar yadda BBC ta ruwaito.

Idan dai za a iya tunawa a daren Talata, Shugaban Kwamitin, Adam Schiff ya fada wa kafar labarai ta MSNBC cewa, kwamitin na kan kammala rahoton. Kuma a daren ne kwamitin ya kada kuri’a kan batun mika rahoton a hukumance ga Kwamitin Shari’a, wanda mambobinsa za su yanke shawara kan ko za su rubuta takardar bukatar tsige Shugaba Trump ko a’a.

Kwamitin Shari’a ya fara  zaman sauraren bahasi shekaranjiya Laraba, ba tare da lauyan Trump yana wurin ba.

Shugaban ya ce ba zai tura wakilai ba “saboda gaba daya rudani ne,” inji shi.