Amsa: Rama abubuwa da dama ne ke kawo ta. Na farko dai akwai gado. Akwai wadanda ko me suka ci a duniyar nan yadda jikinsu yake haka zai kasance ba za su yi kiba ba. Akwai kuma wadanda ramarsu ta rashin cin abinci mai inganci ce, kamar abinci mai gina jiki. Akwai kuma wadanda ramarsu ta wata rashin lafiya ce wadda sauran alamunta ba su riga sun fito fili ba, musamman ma idan da suna da jiki daga baya ne ramar ta zo. Amma a mafi yawan lokuta cututtukan kan zo da sauran alamu. Misalan cututtukan su ne kanjamau, tarin fuka, ciwon daji da ire-irensu.
Ta yaya wanda ke da kibar gado zai ragu? Ni nauyina 80, kuma ina so in ragu.
Daga Muhammad Aminu da Maijidda Katsina
Amsa: Nauyin kilo 80 ba laifi, duk da dai ba ka fadi tsayinka ba, wanda sai an hada su ake gano ko mutum na da kiba ko babu. In ka nemi wallafinmu na baya ko da a yanar gizo ne, za ka ga dabarun da ake yi a rage nauyi.
Ni ma da na ci abinci kafin awa daya kuma sai na ji wata yunwar, ina mafita?
Daga Alhassan Muhammad
Amsa: Shi kuma wannan rashin hada sinadari mai gina jiki, wato protein a abinci shi yake kawo haka. Mun sha zayyano ire-iren wadannan abinci a wannan shafi.
Ni kuma duk lokacin zafi likita sai na yi aman jini, kuma idan na je asibiti akan auna a ce jinina ya yi kasa. Ina neman mafita?
Daga Shu’aibu
Amsa: Ai asibiti iri-iri ne Malam Shu’aibu, inda za a nemi dalilin aman jinin shi ne babban asibiti, inda watakila sai an dauko hoton tumbin cikinka da na farkon hanji da kyamarar nan ta endoscopy, a gano me ke zubar da jini a cikin naka.
Me ke kawo yawan faduwar gaba da tashin tsigar jiki?
Daga Lukman, Shinkafi
Amsa: Akwai ciwon zuciya, akwai ciwon makoko, akwai karancin jini a jiki. Duk wadannan za su iya ba ka irin wadannan alamu. Yana da kyau ka samu a tantance wanne ne a cikinsu.
Ni kuma cikin kashina ke mini ciwo, in kuma yamma ta yi sai jikina ya yi sanyi, kaina ya fara ciwo
Daga Sunusi Muhammad da Murtala kwalli da Abdullahi Tenten
Amsa: Wadannan alamu ne na rashin lafiya da dama, wato daya daga cikin cututtuka da dama kan iya kawo maka haka, tun daga maleriya, tafot, ciwon sanyin kashi ko borin jini, ko karancin jinin da sauran ire-irensu. Ka samu ka je asibiti inda za a yi maka gwaje-gwaje a gano wane ne.
Ni dai ina fama da ciwon jiki a kodayaushe, to sai nake yawan amfani da maganin sa kuzari. Ko hakan zai iya yi mini illa ga lafiyata?
Daga Abdullahi, Makole
Amsa: kwarai kuwa shan magunguna barkatai kuma na tsawon lokaci ba tare da shawarar likitan kwarai ba, ai shi ne yake sa a ce da mutum ya zama dan kwaya. In za ka bi shawarata sai in ce ka daina, sa’annan ka je a bincike jikinka tsaf da jininka a asibiti, a gano me ke sa maka yawan kasala da ciwon jiki.
Ni kuma da na sha magani yake fara yi mini aiki ba jira. Me ke kawo haka?
Daga Maiyaki K/Gora
Amsa: kwarai akwai magungunan da da ka sha su za su fara yi maka aiki, wato ba kowane magani ba ne ke nan da ka sha zai fara aiki.
Ni ina ba da magunguna amma ba karantawa na yi ba. Wacce shawara za ka ba irinmu musamman ta bangaren kwarewa?
Daga Adamu, Zaria
Amsa: To tambayar taka ta zo kan gaba, domin kuwa akwai shirin Gwamnatin Tarayya na daukar dubunnan masu aikin kiwon lafiya da aka fara, wadanda za a ba su horo na shekaru biyu. Amma ina ji sai da shedar kammala karatun sakandare. Ka nemi cibiyar yin rajista mafi kusa da kai, wato shagunan intanet domin su taimaka maka ka yi rajista.
Ko yawan matse bayan gida da fitsari zai iya yin illa ga mutum?
Daga Abubakar, Abuja
Amsa: E, yana iya kawo abin da ake cewa oberflow incontinence, wanda ke nufin wurin ajiyar fitsarin da bayan gidan za su iya tabewa su daina sa maka alamun jin fitsari da bayan gidan. Maimakon mutum ya ji alamar fitsari ko bayan gida, sai dai kawai ya ji sun fara fitowa.
Lokacin sanyi ina yawan fitsari ko da ban sha ruwa ba. Kuma da safe idan na tashi in yawan tofar da miyau. Hakan matsala ce?
Daga Abdullahi RFK da kasim G
Amsa: A’a, wadannan ba matsala ba ne, ana yawan fitsari lokacin sanyi. Shin kuma tofar da miyau yawan goge baki da burushi kafin kwanciya ne zai maka maganinsa.
Ni kuma idan na ga abinci ko abin sha sai miyauna ya tsinke, ya rika dalala. Hakan matsala ce? Kuma mene ne abin yi?
Daga Alhaji A. Kano
Amsa: In dai sai ka ga abinci ne kawai to ba komai, domin ganin abinci yana tsokano masana’antar sarrafa miyau da ke karkashin harshe su fara samar da shi da yawa. Wannan kai za ka nemi dabarar da za ta rika raba ka da shi, kamar yawan burushi ko aswaki a koyaushe, domin suna busar da baki. Amma in dai kai koyaushe bakinka cike da miyau kuma yana dalala, to akwai matsala, sai ka dangana da asibiti
Wane irin amfani barkono ke da shi a jikin dan Adam. Kuma idan ya yi yawa wace illa zai iya sa wa?
Daga Imran, Maiduguri
Amsa: Barkono yana da sinadarin bitaman na rukunin C, kuma yana taimaka wa jiki kona abinci da sauri. Amma idan ya yi yawa zai iya kawo gyambon ciki wato olsa.
Ni kuma kuraje da gishirin fuska sun dame ni, sun yi tabo. Na shafa betamethasone amma ba sauki. A ba ni shawara.
Daga Iman, Jos
Amsa: A’a, maganin shafawa na Benzoyl perodide ake amfani da shi, wasu ma sukan hada da wanda kika fada din. Shi ma dai idan aka yi amfani da shi ba sauki ke nan sai an dangana da likitan fata, wanda zai rubuta wadanda suka fi wadannan karfi.
Ni ina yawan jijjiga kafa, ko a zaune ko a kwance, kai ko barci nake akan gaya mini ina jijjiga kafa. Shin ko wannan rashin lafiya ce?
Daga Nuraddeen M.
Amsa: E, wannan a likitance rashin lafiya ce, wadda ake cewa restless leg syndrome, wato kafar da ba ta hutawa. Masana suna ganin akwai abubuwa da dama masu kawo matsalar, amma dai babban cikinsu shi ne gadon cutar, wato ba za a rasa wani a danginka mai matsalar ba, kuma matsalar tana faruwa ne sakamakon rashin wasu sinadarai da ke aika sako tsakanin kwakwalwa da ita kafar. Idan matsalar tana damunka sosai (domin akwai wadanda matsalar ba ta shafar rayuwarsu ta yau da kullum) ka je babban asibiti bangare neurology su ba ka rana ka ga likita, don akwai magani.