Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da kisan fararen hula sama da 30 da wasu ’yan ta’adda da ake zargin ’yan kungiyar IS masu da’awar jihadi a Yammacin Afirka wato ISWAP, suka yi a Karamar Hukumar Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa da dama daga cikin fararen hular da aka kashe masunta ne.
- Fitaccen dan kasuwa a Kano Sani Yakasai ya rasu
- Gwamnatin Kaduna za ta rabar da shagunan Kasuwar Barci
Wasu fararen hula da aka ce su ma sun sami raunuka daban-daban a yanzu haka ana kula da su a cibiyoyin lafiya.
Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Matthias Schmale, ya yi Allah-wadai da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana damuwa kan lamarin da ya faru a kauyen Mukdolo, da ke Jihar Bornon.
Matthias Schmale ya ce har yanzu ba a san inda wasu fararen hular suka dosa ba, bayan harin da aka kai.
Wani masunci da ya tsallake rijiya da baya ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Laraba ne mayakan na ISWAP sun ritsa su ne ta gabar kogi, suka bude musu wuta inda mutum 35 suka mutu, wasu da dama kuma ba a san inda suka shige ba.
Ya ce “Sun bullo ne daga cikin kungurmin daji a kan babura, suka zagaye mu ta gabar kogin, cewa ‘mun sha jan kunnenku cewa ku daina zuwa nan, amma sai kuka rika gaya wa sojoji inda muke.
“Daga nan suka fara harbi ta kowace kusurwa, mutum uku kacal suka koma Dikwa da ransu, amma ina tabbatar da cewa mutum sama da 35 aka kashe; yanzu haka mutane da yawa ba su dawo garin Dikwa ba.”
Ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Mukdolo da ke kusa da garin Dikwa kuma daukacin ’yan gudun hijirar sun fito ne daga Dikwa.
Da yake tabbatar da labarin harin, Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tayar da kayar baya da kuma sharhi kan sha’anin tsaro a yakin Tafkin Chadi, ya ce an gano gawar mutum 26 daga cikin ’yan gudun hijirar da kungiyar ta kashe.
Ya ce mutum tara daga cikin masuntan da aka kai wa hari sun tsira, amma uku daga cikinsu sun samu raunukan harbi.
Ya bayyana cewa sai da mayakan “Suka sa mutanen kwantawa, suka daddaure su da ragar kamun kifi, sannan suka har suka galabaita, sannan suka bude musu wuta.
“Sojoji sun gano gawarwakin mutum 26 a cikin daji bayan da suka samu labarin abin da ya faru daga sauran wadanda suka tsare,” in ji shi.