Shugaban Kungiyar Paris Saint Germain Sheikh Nasser Al-Khelaifi ya ba da tabbacin dan wasan gaba na kungiyar, Kylian Mbappe zai ci gaba da zama kungiyar.
Al-Khelaifi ya kawo karshen duk wasu zantuka d ke alakanta batun sayar da gwarzon dan wasan gaba na kungiyar yayin hirarsa da jaridar L’Equipe ta kasar Faransa.
- Matasa sun tare gwamna kan kisan mutum 88 a Kebbi
- ’Yan kwallon Najeriya 10 da suka lashe kofi a Turai a bana
Ya ce Mbappe zai ci gaba da taka leda a kungiyar, sannan ba zai bar kungiyar a kyauta ba a kakar wasanni mai zuwa.
Ana rade-radin dan wasan zai iya barin kungiyar da zarar kwantaraginsa ya kare a 2022.
An sha alakanta Mbappe da komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, don maye gurbin Cristiano Ronaldo, wanda ya bar kungiyar shekaru uku da suka gabata.