✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maƙiyan Kano sun hana Abba aiki tsawon shekara guda — Kwankwaso

Kwankwaso ya ce maƙiyan Jihar sun ɗauke hankalin gwamnan ta hanyar kawo cikas ga ayyukansa.

Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi ‘yan adawa a Kano da karkatar da hankalin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na tsawon shekara ɗaya.

Kwankwaso ya yi wannan martani ne, yayin bikin ayyana dokar ta ɓaci kan ilimi a Jihar Kano.

Ya ce, “Bari na fara da taya shi murna a wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamnan ke ayyana dokar ta ɓaci kan ilimi. Gwamnan ya yi aiki kuma duk inda ka saka ƙafarka a jihar za ka ga aikinsa.

“Duk da cewa an ɗauke hankalin gwamnan na kusan shekara guda. Bayan kammala zaɓe, maƙiyan Jihar Kano suka maka shi a kotu – kotun ƙararrakin zaɓe, kotun ɗaukaka ƙara har zuwa kotun ƙoli. Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu buƙatar zuwa wata kotu. Kowa ya san cewa ya ci zaɓe.

“Har ma makiya suna cewa za su yi amfani da ƙarfi don karɓe masa kujera saboda suna da gwamnati. Duk da haka, gwamnan ya dinga aiki kan aiki tare da matsaloli, ba mu san abin da ke faruwa ba, amma gwamnan yana aiki.

“Hakan ya tuna min halin da muka shiga a wa’adina na biyu, watanni biyu bayan rantsar da ni a matsayin gwamna, mun fuskanci hare-haren Boko Haram a masallatai, kasuwanni, ofisoshin ’yan sanda, makarantu da ko ina, amma duk da haka sai muka mayar da hankali don ci gaba da ayyuka.”