Mazauna garin Mpape da ke birnin Abuja, na ci gaba da nuna bacin rai kan dakatar da Hakimin yankin, Alhaji Abubakar Gimba, kan zargin rungumar sauran kabilu da ke da zama a karkashin masarautar.
Aminiya ta samu labarin cewa tun a ranar Juma’ar da ta gabata ce, wata takarda da ke dauke da sa hannun Shugaban Karamar Hukumar Bwari inda yankin yake, ke ta karakaina a yanar gizo, da ke nuna cewa an dakatar da Hakimin, tare da nada Madawakin masarautar, Alhaji Musa Audu, a matsayin Hakimin riko.
- Za mu bai wa bangaren shari’a ’yancin gashin kai — Gwamnoni
- An ceto yarinyar da aka kulle tsawon shekara 10 a Kano
A bara ce wasu da a ke zargin na adawa da salon shugabancin Hakimin, suka kai hari fadarsa tare da kona wani sashenta, inda aka samu nasarar sulalewa da jagoran zuwa wani waje don kubutar da shi.
Wasu jagororin al’umma da ya suka hada da ’yan kabilar Gbagyi, wato kabilar hakimin, da sauran kabilu da ke da zama a garin sun yi tattaki zuwa gidan Shugaban Karamar Hukumar da ke garin Bwari a ranar Talata, inda su ka nuna rashin jin dadinsu a kan matakin da aka dauka.
Haka kuma, tawagar ta bukaci Shugaban Karamar Hukumar wanda ya tabbatar masu da cewa lallai takardar daga wajensa ta fito, da ya janye umarnin tare da mayar wa Hakimin rawaninsa, wanda su ka bayyana a matsayin wanda ya rungumi kowa saboda son a zauna lafiya.
Sun yi zargin cewa wasu ’yan kalilan ne daga cikin ’yan asalin yankin ke da hannu a lamarin wanda a cewarsu hakan na iya janyo tashin hankali.
A jawabinsa, Dokta John Gabaya ya bukaci jama’ar da su zauna lafiya a tsakaninsu, sannan ya ce nan da mako guda zai zauna da zababbu daga cikin jagororinsu don tattauna lamarin.
Daga bisani tawagar ta kai ziyarar girmamawa tare da mika korafi ga sarkin Bwari, Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro, da kuma Esu Bwari, J.P Ibrahim Yaro, kafin su bar garin a cikin ayarin motoci da ke dauke da mutum kimanin dari biyar.