Mazauna garin Kubwa, wani gari da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja, sun koka kan ayyukan masu safarar miyagun kwayoyi.
Wakilinmu da ya ziyarci yankin Kubwa a ranar Alhamis, ya ce wuraren da suka fi yin ƙaurin suna sun haɗa da Junction din 33, Gindin Mangoro da kuma Transfoma.
Dillalan miyagun ƙwayoyin a wannan yanki galibinsu matasa ne, waɗanda ya riska suna hada-hadarsu cikin ƙwarin jiki, ba tare da fargaba ko tsoron hukuma ba.
Wani mazaunin yankin, Patrick Odion ya ce, yana shirin ƙaura saboda yanayin tabarbarewar tarbiyyar yankin.
- Biden ya caccaki Trump kan goyon bayan Rasha a mas’alar NATO
- An yi wa Bajamushe allurar Covid-19 sau 217 ba ta yi tasiri ba
Odion ya ce: “Abin da ke ba ni mamaki shi ne ƙwarin gwiwar waɗannan matasa masu sayar da muggan ƙwayoyin. Suna jin cewa abin da suke yi daidai ne har suna mana barazana.”
Wani mazaunin unguwar mai suna Yusuf Tijjani ya ce: “A makon da ya gabata an kwace wayar matata a ɗaya daga cikin wuraren da yaran nan ke wannan muguwar sana’a.”
Ya ce “Baya ga sayar da ƙwayoyi, suna sata, suna kwace. Don Allah hukumomi su yi wani abu a kai. Na san jami’an NDLEA suna iya ƙoƙarinsu, amma gaskiya su ƙara dagewa.”