Wani dan kasuwa da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, Alhaji Hamisu Rabi’u Mai Manja Saminaka, ya bayyana cewa talakawan da ke zaune a kauyukan kasar nan, a halin yanzu suna cikin wani mawuyacin hali, sakamakon rashin ganin sababbin takardun kudaden da aka sauyawa fasali.
Alhaji Mai Manja ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a ranar Lahadin nan.
- Arsenal ta doke Manchester United a Emirates
- PDP ta bukaci cafke Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi
Ya ce “yanzu ko manyan garuruwa ka shiga, babu sababbin kudaden nan, balle kuma ka shiga kauyuka.
“Wannan matsala ta shafi kowa a Najeriya, talakawa da masu kudi.
“An ce mutane su daina karbar tsofaffin kudade, kuma babu sababbin kudaden.
“Don haka yanzu harkokin kasuwanci sun fara tsayawa a kauyukan kasar nan.
“Domin idan ’yan kasuwa suka karbi tsofaffin kudaden nan, suka kai banki ba a karba.
“Mutane sun fito da tsofaffin kudade daga ko’ina a kauyukan kasar nan.Kuma ga shi babu sababbin kudaden.
“Yanzu ko kudin da mutanen kauye za su yi cefane su kai wa iyalansu babu.
“Don haka ina kira ga Shugaban Kasa da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, su dubi halin da talakawa suka shiga, su kara wa’adin karbar tsofaffin kudaden nan.
“Ina kuma rokon da su dauki matakan samar da sababbin kudaden a ko’ina a kasar nan.