Dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar adawa ta Labour Party (LP), Peter Obi, ya roki ’yan Najeriya su yi wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari uzuri da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) kan sauya kudin kasar.
Peter Obi ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa ranar Lahadi a shafinsa na Twitter.
Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra ya ce ba Najeriya ce kadai ke sauya takardun kudi ba kuma hakan yana da ‘amfani matuka’ na tsawon lokaci.
“Ina rokon ’yan Najeriya su yi wa CBN da Gwamnatin Tarayya uzuri kuma su yi fatan al’umma da kasa baki daya za su ci amfanin sauyin da aka yi.
Sai dai ya yi kira ga CBN da kuma bankunan kasuwanci da su kara kaimi wajen yawaita sababbin takardun kudin ga mutane da wadanda ba su da asusun banki.
A cewarsa, hakan zai rage wahalhalun da ’yan uwansa ’yan kasa ke ciki, musamman talakawa da wadanda ke da nisa da bankuna a kauyuka.
Shi ma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya goyi bayan sauya kudin.
A halin yanzu dai ’yan Najeriya na ci gaba da shiga tasku wajen neman tsabar kudin da za su yi hada-hada da su, inda suke shafe awanni a kan layi kafin su samu daga bankuna.
Za a daina amfani da tsofaffin takardun N1,000 da N500 da N200 daga ranar 10 ga watan Fabarairu, kodayake CBN ya ce za a ci gaba da sauya tsofaffi da sababbi bayan wucewar wa’adin.