Musulmi da dama mazauna yankunan Abuja da ke makwabtaka da jihar Nasarawa sun yi tururuwa sun ketara saboda yin Sallar Idi ranar Lahadi.
Kwanaki kafin Sallar ne dai Ministan Babban Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello, ya bayyana ci gaba da rufe wuraren ibada bayan wani taro da ya yi da shuwagabannin addini wadanda suka gabatar da bukatar bude su.
Hakan ya sa da safiyar ranar Sallah mazauna yankunan Nyanya da Karu da Jikwoyi suka yi tururuwa zuwa yankunan Abatcha Road da Mararaba da Anguwan Albarka saboda samun Sallar.
- Wuraren ibada za su ci gaba da kasancewa a rufe a Abuja
- Dage dokar zaman gida: Kare kai na yi wa mazauna Abuja wahala
Wakilin Aminiya ya tattauna da wasu daga cikin wadanda suka halarci Sallar Idin daga Abuja inda suka koka da rashin ba da damar gudanar da sallar a yankunan Babban Birnin Tarayyar.
Kwai da kwarkwata
Wani wanda ya fito tare da iyalansa, Mallam Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda aka hana gudanar da sallar a Yankin Babban Birnin Tarayya inda ya ce hankalinsa ya ki kwanciya da yin sallar a gida.
“A gaskiya ban gamsu da yin sallar a gida ba ne shi ya sa na fito.
“Kuma tare da iyalina na fito saboda gudanar da sallar tun da an hana a yankunan Abuja.
“Ba mu ji dadin abin da ya faru ba amma kuma mun yi murna tun da mun samu mun yi sallar cikin jam’i”, inji shi.
A nashi bangare, Mohammed Abba Sanda ya bayyana takaicinsa da hana sallar a yankin Abuja wanda hakan ya sa ya yi tattaki zuwa Mararraba da ke jihar Nasarawa.
Wasu sun bi doka
Wadansu mazauna yankin da suka tattauna da wakilin Aminiya ta waya sun bayyana cewa za su gudanar da sallar a gidajensu.
Sarkin Hausawa na yankin Jikwoyi, Musa Yunusa, ya bayyana cewa sun bi umurnin da aka bayar na gudanar da sallar a gida tare da iyalinsa.
A wuraren da aka gudanar da sallar, wakilin Aminiya ya lura cewa ko da yake wasu masallatan sun yi umarni da saka kyallen rufe fuska, amma ba a ba da tazara a lokacin gudanar da sallar ba.