✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maza biyu za su auri mace daya a kasar Kenya

Wasu mazaje a kasar Kenya na shirin auren mata daya. Matar dai ta saba hulda da su fiye da shekara hudu, kuma ta ki zabar…

Steven Mwendwa, daya daga cikin mutanen da suka kulla yarjejeniyar auren mace dayaWasu mazaje a kasar Kenya na shirin auren mata daya. Matar dai ta saba hulda da su fiye da shekara hudu, kuma ta ki zabar mutum daya daga cikinsu. Wadannan mazaje, Sylbester Mwenda da Elijah Kimani sun yanke yarjejeniyar zama da wannan mata a matsayin mazan aure, inda suka amince za su kula da ’ya’yan da ta haifa.
daya daga cikin wadanda ke shirin auren matar, Mista Mwenda ya bayyana wa BBC Landan cewa, yarjejeniyar auren da za su kulla, za ta gindaya wa kowa iyakarsa, ta yadda za a samu zaman lafiya. “Ita wannan mata tamkar mai hura wasa  ce da ke tsaye a tsakiyar fili. Za ta iya cewa ni take bukata ko kuma abokin tarayyata,” inji shi.
dan sandan al’umma ne, Adhalah Abdulrahman, da ya gansu suna fada a kan wannan mata, sai ya ba su shawarar su aureta gaba dayansu. Sai dai lauyoyin kasar sun nuna cewa irin wannan nau’in aure da wuya ya yiwu, domin ya saba wa addininsu da al’adarsu. Kuma babu wata al’umma a kasar Kenya da ke gudanar da irin wannan aure, kamar yadda Dabid Okwembah ya bayyana wa BBC a birnin Nairobi.
Ita kuwa Lauyar dokokin kula da iyali, Judy Thongori, ta bayyana wa jaridar Daily Nation cewa doka ba ta fito karara ta hana maza da yawa auren mace daya ba.
“Dokokinmu na Kenya ba su yi magana a kan irin wannan auren ba, don haka kafin wannan nau’in aure ya samu amincewa a Kenya, sai a gudanar da shi kan dokokin da ke zayane ko bisa tsarin auratayya ta al’ada. Abin tambaya a nan, shi ne, ko wadannan mutanen sun fito ne daga al’ummomin da ke da al’adar maza masu yawa su auri mace guda?”