✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayaƙa fiye da 100 sun mutu a rikicin ISWAP da Boko Haram

Ana cikin yanayi mai cike da sarkakiya kasancewar kungiyar ISWAP na shirin ɗaukar fansa.

Rahotanni na cewa mayaƙa fiye da 100 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani ƙazamin faɗa da aka gwabza tsakanin ƙungiyar ISWAP da Boko Haram a gabar Tafkin Chadi.

Ƙwararren mai sharhi kan al’amuran yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, ya ce ƙungiyoyin mayaƙan biyu sun yi ba-ta-kashin ne a yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno.

Makama, ya ce aƙalla mayaƙa 100 daga ɓangarorin biyu ne aka kashe a rikicin da ya ɓarke a tsibirin Toumbun Gini da ke Karamar Hukumar Abadam kwanaki 10 da suka gabata.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa jagoran mayaƙan Boko Haram, Buduma na Bakoura wanda aka fi sani da Abu Umaima, sun ƙaddamar da harin ba-zata a kan mayaƙan ƙungiyar ISWAP da ke hedikwatarsu ta Toumbun Gini.

Majiyar ta ce harin na ba-zata ya janyo wa ƙungiyar ISWAP asarar mayaƙa aƙalla 90 yayin faɗan mai tsanani da suka gwabza.

Kazalika, mayaƙan na Boko Haram bangaren sun ƙwace makamai da kayan aiki a yayin yakiyn inda daga bisani suka karɓe iko da yankunan da ke ƙarƙashin ISWAP da suka haɗa da Toumbun Kare da Toumbun Rogo a Ƙaramar Hukumar Abadam.

Wannan karon-batta ta baya-bayan nan dai na cikin jerin munanan hare-hare da aka yi tsakanin ɓangarorin da ke gaba da juna.

Ana iya tuna cewa, a ranar 6 ga Yuli, 2024, mayaƙan Boko Haram sun kai wani ƙazamin hari a sansanin ISWAP da ke Kwatar Shalla Shuwari, inda suka kashe mayaƙan ISWAP 16 tare da kama jiragen ruwa 8, da makamai da dama, da kuma maƙudan kuɗaɗe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, kayayyakin da aka mayaƙan suka ƙwato an kai wa shugaban Boko Haram Abu Umaima a sansanin Alli Modulla da ke Diffa a Jamhuriyar Nijar.

Har ila yau, a wata arangama da aka yi a baya a Dawashi Kwalta tsakanin ɓangarorin biyu, an kashe ’yan ta’addan ISWAP sama da 20, wasu kuma suka nutse a ruwa a ƙoƙarin tsallake kogi.

Rahoton na Zagazola ya ƙara da cewar, a halin yanzu ’yan ta’addan Boko Haram ne ke iko da yawancin sassan yankin, sai dai ana cikin yanayi mai cike da sarkakiya kasancewar kungiyar ISWAP na shirin ɗaukar fansa.