Akalla mutum biyu sun bakunci lahira bayan mayakan Taliban ta bude wuta a kan wasu masu gangamin ranar samun ’yan kai a birnin Asadabad na kasar Afghanistan.
A Jalalabad ma mayakan Taliban sun raunata wani saurayi da wani dattijo a lokacin suka bude wuta a kan wasu masu gudanar da gangamin ranar ’yancin da ke daga tutar kasar.
Hakan na zuwa ne bayan Taliban ta sauya tutar kasar, jim kadan bayan ta dare a kan karagar mulki bayan da ta kwace mulki daga gwamnatin Shugaba Ashraf Ghani wanda ya tsere zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Rana ta biyu ke nan da ’yan kasar ke kalubalantar matakin na Taliban, inda aka samu zanga-zanga kan sauya tutar kasar a wasu sassan kasar.
Wakiliyar kafar labarai ta Al Jazeera a birnin Kabul na kasar Afghanistan, Charlotte Bellis, ta ce: “A Kabul ma an samu daidaikun zanga-zanga kan tutar kasar, inda mutane, ciki har da mata dauke da tsohuwar tutar kasar suke tafiya suna wuce mayakan Taliban suna cewa: ‘Tutarmu ce asalinmu.’”
A halin yanzu dai kasashe na ci gaba da kwashe mutanensu da wasu ’yan Afghanistan daga filin jirgin sama da ke birnin na Kabul.
A ranar Laraba, Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce dakarun kasarsa za su ci gaba da zama a Afghanistan har sai an gama kwashe Amurkawan da ke can ko da zuwa bayan wa’adin ranar 31 ga Agusta da aka dibar wa sojojin ne.
A halin yanzu dai ana ganin Taliban na neman samun karbuwa a wurin mutanen Afhanistan inda take nuna musu sassaucin ra’ayi sabanin yadda ake ganinta mai tsattsauran ra’ayin addini a baya.
A wannan karon an ga mayakan Taliban cikin murmushi suna daga wa ’yan jarida hannu, har ana daukar hotunan selfie da su a kan tituna, suna kuma yin hira da mata ’yan jarida.
Ana ganin hakan wani salo ne na kyautata alakar kungiyar da mutanen kasar ta hanyar nuna musu cewa yanzu tana da sassauci.