Wasu da ake zargin ’yan ta’a’addan kungiyar ISWAP ne, sun tare matafiya a kan hanya inda suka raba musu kyautar makudan tsofaffin kudade a Jihar Borno.
Wakilinmu ya ruwaito cewar lamarin ya faru ne a kauyen Mairari da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno a Karamar Hukumar Guzamala ta Jihar.
- NAJERIYA A YAU: Irin Tarbar Da Kanawa Suka Yi Wa Buhari
- Rufa-rufa Emefiele ya yi wa Buhari kan sauya kudi —Doguwa
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewar mayakan sun yi shiga irin ta sojoji dauke da bindigu lokacin da suka yi rabon kudin.
Wani mazaunin yankin mai suna Bakura Ibrahim, ya ce mayakan sun tsaya karkashin wata bishiya dauke da manyan jakunkunan kudi.
“Mun bar Monguno da misalin karfe 12:00 na rana inda muka nufi Mairari, kuma babu shingen bincike a kan hanyar.
“Sun tare mu suka tambaya ko Maiduguri za mu je. Nan take suka fara raba mana kudi, sai da suka bai wa kowa na cikin motar kyautar 100,000,” in ji Bakura.
Wata majiyar kuma ta ce, “Sun ce mana idan za ku iya zuwa banki ku sauya kudin to ku je, Allah ya sa ku amfana.”
Wannan dai na zuwa ne bayan wa’adin da Babban Bankin Najeriya (CBN), ya bayar na daina amfani da tsofaffin takardun kudi.