✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan ISWAP 70 sun mika wuya a Borno

Sun mika wuya sakamakon yunwa da ta addabe su, gami da luguden bama-bamai a maboyarsu

’Yan ta’addar kundiyar ISWAP da Boko Haram 72 ne suka mika wuya ga sojojin rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) a Karamar Hukumar Dikwa ta Jihar Borno.

Mayakan su 72 sun mika wuya ne sakamakon yunwa da ta addabe su, gami da luguden bama-bamai da sojojin hadikin gwiwa suka matsa da kaiwa maboyarsu a Dajin Sambisa da kuma Yankin Tafkin Chadi.

Bayanin hakan ya fito ne daga kwararren masanin yaki da tayar da kayar baya, Zagazola Makama, inda ya ce, “Wasu daga cikinsu sun yi ikirarin cewa su manoma ne kuma suna makale a lungu da sako tare da ’yan ta’adda.”

Da yake bayani a Maiduguri, hedikwatar Jihar Borno, Zagazola ya ce, yawancin ’yan ta’addar da suka mika wuya tare da iyalansu suna farin cikin sake shigar da su cikin yankunan da sojoji suka kwato.

Ya bayyana cewa dakarun hadin gwiwar sun karbi tubabbun ’yan ta’addar ne a ranar Larabar da ta gabata.

Wani babban jami’in leken asiri na soji ya shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa za a bayyana sunayen tubabbun ’yan ta’addar, kafin a mika su domin sauya tunaninsu da kuma komawa cikin al’umma ba tare da samun wani tarnaki ba.