Akalla mutum daya aka harbe murus yayin da aka yi awon gaba da matafiya da dama a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a wani hari da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram sun kai da Yammacin ranar Juma’a.
Aminiya ta samu ce mayakan haramtacciyar kungiyar sun far wa matafiya da misalin karfe 6 na Yamma a kauyen Kondiri kusa da garin Jakana a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, inda suka yi awon gaba da dukkan fasinjojin da ke cikin wata motar haya tare da jikkata mutum hudu.
- Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 10 a Somaliya
- Coronavirus ta sake kashe karin mutum 11 a Najeriya
A cewar wani shaidar gani da ido, Modu Usman wanda da kyar ya tsallake rijiya da baya, ya ce maharani sun yi shigar kakin soja tare da wasu motoci biyu kirar Toyota Hilux a gefen hanya dauke da manyan bindigogi.
“Allah ne ya cece mu, direban motar mu yana da kyakkyawar masaniyar wannan hanyar, don a yayin da muke tunkararsu tuni sun cafké motoci biyu da ke gabanmu wanda hakan ya sanya sauran direbobi suka ka rika juya motocinsu zuwa daji a yayin da maharan suka fara harbi.
“Sai muka dawo wani gari da ake kira Benishek inda a nan muka kwana, da safiyar yau mun ga motoci hudu ciki har da wata babbar mota mallakar Kamfanin siminti na Dangote da aka kona,” inji Usman.
Wata majiya ta ’yan banga ta kuma tabbatar da faruwar lamarin da cewa mutum daya ne mutu sannan wasu hudu sun jikkata a yayin da maharan suka yi wa matafiyan kofar-rago.
Sai dai majiyar ta ce abin takaicin shi ne maharani sun yi garkuwa da wasu fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba.
Majiyar ta ce an shigar da korafi a kan lamarin ga Ofishin ’yan sanda na Auno.
Kazalika, wani harin kunar bakin wake da ake zargi kungiyar Boko Haram ce ta kai garin Konduga ranar Juma’a ya kashe mutum biyar kuma wasu da dama sun jikkata.