✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram sun tare hanyar Damaturu-Maiduguri

Mayakan kungiyar Boko Haram tare babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri inda suka kone motoci da dama.

Mayakan kungiyar Boko Haram tare babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri inda suka kone motoci da dama.

Rahoton da Aminiya ta samu ya nuna ’yan kungiyar Boko Haram sun tare motoci a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri suka banka musu wuta, ciki har da manyan tankokin dakon man fetur.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun tare hanyar ne kusa da kauyen Lawan Mainari a yankin Mainok da ke Karamar Hukumar Kaga a Jihar Borno — Tsakanin wurin da suka tare da kauyen bai wuce kilomita 30 ba.

Wani direban mota da ya sha da kyar ya shaida wa wakilinmu a garin Damaturu cewa, maharan sun kafa shingen tare matafiyan ne da sanyin safiyar Litinin, suka rika banka wa motocin matafiyan wuta ba kakkautawa.

Direban ya ce ganin hakan ne Allah Ya ba shi sa’a da ya hango su daga nesa ya juya motarsa da kyar ya koma da baya shi da wasu masu abubuwan hawa.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin jami’an tsaro lamarin ya ci tura sai dai nan gaba.

Game da ko ya maharan sun yi garkuwa da wasu matafiya, direban ya ce shi daga nesa ya hango su don haka ba shi da wata masaniya.

Sai dai ya ce a lokacin da ’yan bindigar suka wuce sun dawo za su wuce, sai suka ga wata motar da ba a banka wa wuta ba akwai wasu yara ciki a zaune.

Amma babu iyayen su wadda hakan a ganin sa akwai yiwuwar maharan sun tafi da wasu matafiyan.