Wasu ’yan bindiga da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun kai hari wani kauye da ke yankin Arewa mai nisa a Kasar Kamaru.
Harin kamar yadda Gidan Rediyon Faransa (RFI) ya ruwaito, ya ce ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutum uku ciki har da mata biyu.
- An kashe mutum 137 a harin Jamhuriyar Nijar
- Batan N4bn: An maka Shugabannin Majalisun Tarayya a kotu
Wani Kansila da ke wakiltar yankin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mayakan sun kai harin ne a kauyen Bla-Goussi Torou da ke kan iyaka da kasar Najeriya.
Aminiya ta samu cewa wannan sabon hari na zuwa ne a daidai lokacin da wani makamancinsa ya auku wanda mayakan Boko Haram suka kai garin Wulgo a Najeriya har ya yi ajalin wasu sojojin Kamaru guda biyu.
A tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, wani sojan Najeriya ya ce, “Akwai sojojin kasar Kamaru guda biyu da aka kashe bayan musayar wuta ta kusan tsawon minti 40 da ’yan mayakan Boko Haram.”
Tun yayin da kungiyar Boko Haram ta daura damarar ta’addanci a shekarar 2009, rayukan sama da mutane 36,000 sun salwanta sannan ya raba sama da mutum miliyan biyu da muhallansu kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar.