✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Boko Haram sun kashe mutum 12 a Borno

Sun kai hari kan al’ummar Tsiha da ke kusa da Shikarkir inda suka kashe mutane uku tare da sace wata budurwa.

Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sanye da kakin soji sun kashe mutane 12 tare da yin garkuwa da daya a kauyukan Gatamarwa da Tsiha da ke Karamar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.

Harin na baya-bayan nan dai ya zo ne makonni biyu kacal bayan da ‘yan ta’addan suka kai makamancin harin a garin Chibok, inda suka kashe mutane biyu tare da wawashe kayan abinci a wasu gidaje sannan suka kona su.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso Kenneth, ya tabbatar da faruwar harin da cewa har sun gano gawarwaki 12.

“’Yan bindigar sun yi harbe-harbe kan mai uwa da wabi a yankunan biyu. Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 12 sannan biyu sun samu raunuka,” inji shi.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda da sauran shugabannin tsaro sun bayar da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Aminiya ta tattaro cewa ‘yan ta’addan sun afka wa al’ummar Gatamarwa ne da misalin karfe 5 na Yammacin ranar Litinin a yayin da ake bikin sabuwar shekara.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu a ranar Talata cewa, ‘yan ta’adda dauke da makamai sun afka wa yankunan al’ummar da dama.

“’Yan ta’addan wadanda ke dauke da bindigogi kirar AK-47, sun zo ne a kan babura da wasu a cikin motocin Hilux, inda suka bude wuta kan masu jimami da suka dawo daga Gatamarwa.

“Daga baya sun kai hari kan al’ummar Tsiha da ke kusa da Shikarkir inda suka kashe mutane uku tare da sace wata budurwa. Sannan sun kona gidaje bayan sun wawashe kayan abincinsu,” inji shi.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar hare-hare a Jihar Borno, inda ko a makonnin da suka gabata aka daina samun wutar lantarki a Borno da Yobe bayan ’yan ta’adda sun lalata wata babbar cibiyar samar da wutar lantarki mai karfin 33KVA da ta hada jihohin biyu.