✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram sun kai hari Maiduguri

Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin dakarun soji da mayakan Boko Haram.

Mazauna gari sun rika tserewa daga gidajensu yayin da aka ji karar abubuwan fashewa da dama da yammacin Talata a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, karar abubuwan fashewar masu karar gaske da dode kunnuwa ta rika tashi a yankin filin Polo na Jiddari da misalin karfe 5.55 na yammacin Talatar.

Aminiya ta ruwaito cewa, ana ci gaba da musayar wuta tsakanin dakarun soji da wasu da aka zargi mayakan Boko Haram ne a yankin Molai da Jiddari.

A cewar wakilinmu, “an ji kara mai karfin gaske har sau uku ta abubuwan fashewa a Maiduguri.”

“Ana ci gaba da harbe-harbe, mazauna gari na ci gaba da tserewa daga mahallansu zuwa Damboa da kuma tsohuwar GRA.”

Majiyar rahoton ta ce mayakan sun kona gidaje da dama yayin harin da suka kai ana gab da buda baki.