Wasu ‘yan bindiga da ake zargi mayakan Boko Haram ne, sun kai wani sabon hari a Karamar Hukumar Geidam ta Jihar Yobe.
Wata majiya daga Geidam ta shaida wa wakilinmu cewa, Boko Haram din sun kai hari garin ne bayan sallar Magriba a ranar Talata.
- ’Yan bindiga sun sako Mataimakin Shugaban Hukumar Shige da Fice
- An kai mutum 25 gidan yari saboda karya dokar COVID-19 a Kano
- Wanda ya jagoranci sace Daliban Kankara ya mika wuya
- Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Yobe
“Yanzu haka mun buya a cikin gida, mun gode wa Allah kowa namu na cikin gida,” a cewar majiyar.
Wani mazaunin garin, Muhammad Nura, shi ma ya tattauna da wakilinmu ta waya cikin firgici da dimuwa inda ya bayar da shaida cewar kowa ya nemi mafaka don tsira da rayuwarsa.
“Ban san me zan ce ba muna bukatar addu’arku saboda harin da suka kawo na baya har yanzu ba mu manta da shi ba kuma ga shi yanzu kasa da wata daya sun sake kawo wani harin.
“Jami’an tsaro na iya kokarinsu saboda muna iya jiyo karar harbin bindigarsu, amma duk da haka gwamnati ya kamata ta yi wani abu kafin su kore mu daga garinmu,” in ji Nura.
Sai dai an gaza samun jin ta bakin rundunar soji da jami’an ‘yan sanda yayin tattara wannan rahoto.