Majiyoyi da dama sun tabbatar wa da Aminiya cewa ’yan ta’addan da suka guje wa karan-batta da sojoji a Jihar Zamfara, sun fara yin sansani a wasu kauyukan Jihar Kaduna guda biyu.
Kauyukan dai sun hada da Saulawa da kuma Damari, dukkansu a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kadunan.
- Yadda ake hada baki da ’yan uwa a sace mutane a Zariya
- Katse layukan waya: Zamfarawa da Katsinawa Na Kaura Daga Gida
A cewar majiyoyin, daruruwan mayakan, wadanda ake kyautata zaton ’yan kungiyar Ansaru ne sun rika shiga garuruwa a kan babura, kafin daga bisani su kafa tuta a ciki.
Damari da Saulawa dai na daga cikin kauyukan Birnin Gwari da ’yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka.
A shekarun baya dai, rahotanni sun ce an taba cimma wata yarjejeniya tsakanin mutanen garuruwan da ’yan ta’addan, inda aka kyale mutanen su yi noma, su kuma ’yan bindigar aka kyale su su ci kasuwa tare da jama’ar gari.
Sai dai yarjejeniyar ta wargaje a watan Fabrairu bayan da ’yan bindigar suka kai hari yankuna da dama sannan suka karkashe mutane.
Da yake zantawa da wakilin Aminiya, wani jagoran matasa a yankin Dogon Dawa na Karamar Hukumar ya ce tuni wasu mazauna garin na Damari suka fara janye jikinsu suna komawa Zariya, wasu kuma suka kai iyalansu can, in ban da maza da suka zauna domin yin noma.
“Sama da mayaka 400 sun shigo ranar Talata sannan sun karbe iko da Saulawa da Damari, sun karkafa tutoci a ciki. Ba su kai wa kowa hari ba, amma mutane sun tsorata sai guduwa kawai suke yi,” inji shi.
Wani babban jami’in tsaro a Jihar ya shaida wa Aminiya cewa rahoton kwararowar ’yan ta’addan ya iske su, inda ya ce kamata ya yi a ce aikin fatattakar tasu ya hada har da makwabtan Jihohi.
“Abin da muka yi tsammani da farko shi ne yayin da ake ragargazarsu a Zamfara, za a girke jami’an tsaro a muhimman wurare don hana su tsallakawa makwabtan Jihohi, amma abin takaicin ba haka ba ne,” inji shi.
Sai dai yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Samuel Aruwan ya ci tura saboda bai amsa kiran waya ko sakon kar-ta-kwana da na WhatsApp ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton
Sai dai Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige ya ce rundunarsu ba ta sami rahoton kafa tutar a Damari da Saulawa ba, amma ya ce suna aiki da sauran hukumomin tsaro wajen magance kalubalen.