✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayaƙa 100 sun mutu yayin arangamar ISWAP da Boko Haram

Lamarin na zuwa ne yayin da ISWAP ke shirye-shiryen tunkarar Boko Haram domin a yi ta ta kare.

Wani ƙazamin rikici tsakanin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya na Boko Haram da ISWAP ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mayaƙa 100 a gabar Tafkin Chadi.

Wata majiyar tsaro daga bakin sanannen mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ce ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a makon da ya gabata.

Majiyar Zagazola ta ce sama da mayaƙa 100 na ɓangarorin biyu sun kwanta dama a yayin arangamar.

A cewarta, tun daga ranar 18 ga watan Afrilu zuwa 24 ga watan Afrilu an yi arangama tsakanin ɓangarorin Boko Haram da ISWAP a kogin Tumbum, inda ISWAP ta ƙara samun gindin zama tare da fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram da ke gaba da juna.

Jim kaɗan bayan ISWAP ta samu sabon makami daga ƙasar Mali, ta hanyar Nijar zuwa Dogon Chukwu Kangarwa, ta sake ƙaddamar da yaƙi, inda ta bayar da wani kakkausan umarni ga mayaƙanta da su kakkaɓe ‘yan ƙungiyar ta Boko Haram na Buduma gaba ɗaya a ranar 18 ga watan Afrilu.

Kafin wannan arangama, Ƙungiyar ta Boko Haram ta kori mayaƙa da dama daga sassan kogin Nijar da ke saman kogin Neja, inda suka kai farmaki a Kukawa a Borno, yayin da wasu gungun mayaƙa ɗauke da makamai suka koma kan iyakokin Najeriya da Kamaru, inda suka mamaye Dawashi, Dabar Wanzam, Kiri, Bulla a Kukawa da Lokobili da Kandahar a Kamaru.

A ɓangarenta, ISWAP ta hau kan jiragen ruwa 20, inda ta kai mayaƙanta kimanin 130 zuwa Doron Kirta Wulgo da ke iyakar Najeriya da Kamaru.

Wasu ƙarin mayaƙan ISWAP sun iso daga Kwalaram, yayin da wasu kuma suka shigo daga Ngala da Marte, a shirye-shiryen babban taronsu na ƙoƙarin kai farmaki kan Boko Haram don a yi ta ta ƙare.