Allah ya yiwa shahararran mawakin nan na Hausa, Alhaji Hassan Wayam mai wakar Kukuma Easy rasuwa a cikin daren jiya.
An yi jana’izarsa yau Asabar da misalin karfe 9:00 na safe a gigansa da ke layin Zomo a Unguwar Falladan da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya.
Tarihi ya nuna cewa a cikin shekarar 1956 aka haifi Alhaji Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda, wanda kuma ake kira Bakin Ruba, a kasar Maradun ta Jihar Zamfara.
Mahaifin sa, Malam Muhammadu Babarbare ne mai sana’ar sassaka yayin da a wasu lokutan ya rika yi wa Fulani kidan kotso jefi-jefi.
Bayan Hassan ya kara wayo, sai ya koma garin Mayanci da ke kusa da Gusau, ya zama yaron kanikawa.
Kasancewar Mayanci bariki ce sosai a wancan lokacin, ga karuwai da ‘yan caca da sauran ‘yan duniya, a nan ne sha’awar sa da kade-kade ta yi zurfi, musamman kidan kukuma.