A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa, Alhaji Abdu Wazirin danduna rasuwa.
An yi jana’izar marigayin shekaranjiya Laraba.
Ya rasu a asibitin Nassarawa da ke birnin Kano, inda aka kwantar da shi a sakamakon ciwon cikin da ya dade yana damunsa.
dan marigayin Muhammad Sagir ya ce: “Har ma ana shirin yi masa tiyata, sai Allah Ya yi masa rasuwa.”
Ya mutu yana da shekara 86 a duniya, ya bar mata biyu Hasiya da A’isha da ‘ya’ya takwas , maza hudu, mata hudu.
Marigayin dan asalin garin Yaryasa ne da ke karamar Hukumar Tudun Wadan dankadai a Jihar Kano, daga baya ya koma unguwar Sheka da ke cikin Kano da zama har zuwa mutuwarsa.
Marigayin dan gidan malamai ne, ya kuma hardace kur’ani.
A cikin wakokinsa akwai ‘Sarkin karaye Abubakar’ da ‘Duniya Da Wuyar Zama’ da ‘Tsakanin dan Adam da Kudi’ da kuma bakandamiyarsa wakar marigayi ‘Sarkin Kano Sunusi’.
Mawaki Abdu Wazirin dan Duna ya rasu
A ranar Talatar da ta gabata ne Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa, Alhaji Abdu Wazirin danduna rasuwa.An yi jana’izar marigayin shekaranjiya Laraba. Ya…
