✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maulidin Nyass: Al’amura sun tsaya cik a Abuja

Dandazon al’ummar Musulmi mabiya Darikar Tijjaniya daga ciki da wajen Najeriya ne suka hallara a filin wasa na Kasa da ke Birnin Tarayya, Abuja inda…

Dandazon al’ummar Musulmi mabiya Darikar Tijjaniya daga ciki da wajen Najeriya ne suka hallara a filin wasa na Kasa da ke Birnin Tarayya, Abuja inda suka halarci taron Maulidin Shehu Ibrahim Nyass karo na 119 da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Taron wamda ya gudana a karkashin jagorancin jagorar Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya jawo tsayawar al’amura a wasu sassan birnin, inda mutane suke shafe awa biyu zuwa uku a tafiyar da ba ta wuce minti 15 ba.

Dandanzon masu halartar Mauludin ya tilasta toshe gaban manyan shaguna da dama da ababen hawa, tare da tsayawar zirga-zirgar motoci a babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da ta taso daga mahadar Berger zuwa yankunan Area 1 da Area 2 da filin wasan ke kan hanyarsu da kuma wasu sassa na hanyar zuwa filin jirgin sama na Abuja.

Tun ranar Juma’a ce mabiya Darikar Tijjaniyyar suka hallara a Abuja inda wadansu daga cikinsu suka rika kwana a kan tituna. Yayin da filin wasan ya cika makil da jama’a, sannan a ranar Asabar an rika samun tureneniya wajen shiga filin wasan lamarin da ya sa aka kakkarya katangar waya a wasu sassa na filin wasan.

Bikin Maulidin an fara shi ne da gabatar da laccoci da jawabai na mako guda da ake kira “Makon Shehu” wanda aka yi a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja mai taken: “Rayuwar Shehu Ibrahim Nyass, Gwagwarmaryarsa da Bayanin Darikar Tijjaniyya da irin Gudunmawar da ya bayar ga ci gaban addinin Musulunci.

A jawabinsa lokacin bude taron Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce ana shirya taron ne domin a nuna karfin Musulunci a kuma nuna hasken Musulunci kuma a girmama bawan Allah, Shehu Ibrahim.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a lokacin taron ana duba irin koyarwar da Shehu Ibrahim ya yi ne lokacin da yake raye a kuma amsa tambayoyin dalibai da ’yan uwa da nufin kara ilimantar da al’umma da kuma kara dankon zumunci.

Ya karanto ayoyi daga cikin Alkur’ani Mai girma inda ya ce Allah ne Ya yi umarni a girmama alfarmar da Ya girmama, kuma Ya ce “Ubangiji Ya ce girmama abubuwan da Allah Ya girmama yana daga cikin tsoron Allah. Sheikh Dahiru Bauchi ya ce: “Ina bai wa al’ummar Musulmi shawara mu hada kanmu, mu so junanmu, mu taimaki junanmu. Kada mu taimaki masu neman watsa jama’a, duk mai neman kafirta Musulmi yana neman watsa jama’ar Musulmi ne, ya nuna wa duniya cewa ba ya son jama’ar Annabi Muhammadu su yi yawa, ya fi son jama’ar Shaidan su yi yawa.”

Cikin malaman da suka gabatar da laccoci akwai Sheikh Abdullahi Doso da Khadi Mustafa Umar Suleiman da Sayyid Mustafa Adinga da Khalifan Sheikh Muhammad, Hafiz Ahmad Muhammad Hafiz daga kasar Masar da Dokta Abdullahi Ahmad Tijjani daga Masar da Alhaji Yusuf Abdurrahman daga Malaysia wanda ke zaune a Amurka, inda suka zaburar da Musulmi kan neman ilimi da yin ayyukan ibada da nuna soyayya ga Allah da Manmzonsa da zababbun bayinsa da al’ummar Musulmi baki daya.

Malaman sun ambato littattafai 75 da Shehu Ibrahim ya rubuta lokacin da yake raye inda suka ce littattafan suna karantar da tsoron Allah da son Allah da biyayya ga Allah da ManzonSa da kuma wayar da kan Musulmi kan ilimomi a fannonin daban-daban na rayuwa.

Laccocin wadanda aka shafe kwana uku ana gabatarwa daga Laraba zuwa Juma’a an rufe su ne da Zikirin Juma’a a Babban Masallacin Kasa inda Sheikh Dahiru Bauchi da sauran manyan malaman da suka zo daga kasashen duniya suka halarta.

Lokacin da Sheikh Dahiru Bauchi ya isa filin wasa na kasa sai filin ya kaure da zikiri da kabbara, yayin da Shehun Malamin ya liko ta samar mota yana zagaya filin yana yi wa jama’a maraba tare da addu’a lamarin da ya kara zaburar da mutane suka rika tururuwa zuwa wurin da yake. Dandazon jama’ar da suka yiwo kan Shehun Malamin ya sa Shehi bai iya isa wurin da aka shirya zai zauna ba sai da aka zagaya da shi ta baya.

A sakonsa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari  ya bayyana farin cikinsa kan yadda ya ga dimbin masoya Manzon Allah (SAW) sun yi cincirindo a wajen taron Maulidin inda suke nuna soyayyarsu da shauki da ambaton Allah da addu’o’in zama lafiya ga Najeriya.

Shugaba Buhari wanda Ministan Birnin Tarayya, Abuja, Muhammad Bello ya wakilce shi ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da yin addu’a domin samun zama lafiya mai dorewa a kasar nan. Kuma ya hori ’yan Najeriya su kauce wa aikata duk wani mummunan abu da bai dace ba, sannan ya nanata aniyar gwamnati na samar da tsaro a kasa da kuma kawo sauki ga rayuwar ’yan Najeriya.

Manyan bakin da suka halarcin Mauludin akwai wakilin Shugaban Kasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Alhaji Muhammad Musa Bello da Halifan Tijjaniyya a kasar Masar Sheikh Muhammad Ahmad Al-Hafiz, da Sayyadi Muhammadu Habib Sheikh Ahmad Dam daga Senegal da manyan malamai daga kasashen Senegal da Mauritaniya da  Mali  da Aljeriya da Amurka da Sudan da Ghana da Kamaru da Nijar da sauransu.

Shugaban Kwamitin Shirya Laccoci da Mauludin Sayyadi Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi ya shaida wa Aminiya cewa an yi Maulidin Shehu Ibrahim a Abuja ne a bara da bana saboda kasancewarta a tsakiya don a sawwaka wa masu zuwa daga ko’ina a fadin kasar nan. Ya ce kuma Abuja ne ke da isassshen filin da zai iya daukar dimbin mutanen da ke zuwa Maulidin cikin sauki.

Ya ce ko a badi akwai ’yan uwa da suke da sha’awar a yi shi a Abuja saboda dalilan da aka ambata. Ya ce sai dai saboda soyayyar alherin yin Maulidin akwai ’yan uwa da yawa masu sha’awar a kai garuruwansu da jihohinsu, saboda haka idan lokacin ya matso in aka yi shawara za a fadi inda za a yi bayan an samu izini daga Sheikh Dahiru Bauchi.