✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsin lamba: Kasashen rainon Faransa sun dakatar da kasar Mali

Kungiyar Kasashe Rainon Faransa (OIF) ta dakatar da kasar Mali daga cikinta a wani karin matsin lamba da kasashen duniya ke wa sojojin da suka…

Kungiyar Kasashe Rainon Faransa (OIF) ta dakatar da kasar Mali daga cikinta a wani karin matsin lamba da kasashen duniya ke wa sojojin da suka yi jurin mulki a kasar.

A taron gaggawar OIF na ranar Talata, kungiyar ta yi ittifakin hada kai domin taimakon fararen hula da kuma dawowar mulki demokradiyya a Mali.

Tuni dama manzannin Kungiyar Raya Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) suka kasa cimma matsaya da masu juyin mulkin game da lokacin da kasar za ta koma hannun farar hula.

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya ce ba ya bukatar a mayar da shi kan mulki sabanin bukatar ECOWAS wadda ke kan gaba wajen nemo mafita ga rikicin, wadda ta kuma dakatar da Mali daga cikinta saboda juyin mulkin da sojojin suka.

OIF ta bukaci sojojin da su saki Shugaba Keita da ya sauka daga mukaminsa bayan boren sojojin, domin kawar da zubar da jini a kasar.

Sannan a gaggauta kafa “gwamantin rikon kwarya ta farar hula a kasar”, inji OIF wadda ke shirin tura wata babbar tawagarta zuwa Mali nan gaba.

Kasashen duniya sun yi tir da bore da kuma juyin mulkin da sojojin suka yi a ranar 18 ga watan Agusta, 2020.

An zabi Keita a 2013 a lokacin da ake ganinsa a matsayin mai kawo hadin kai a kasar da ke fama da matsaloli.

An sake zabar sa a 2018 amma gwamnatinsa ta kasa magance rikicin mayakan jihadi baya ga na kabilanci da suka kara durkusar da arzikin kasar.

Korafe-korafen zaben ‘yan majalisar kasar sun kawo jinkiri bayyana sanar da sakamakon zaben na watan Afrilu, wanda hakan ya kara shafa masa kashin kaji, har da ta kai ga zanga-zanga da hambarar da gwamantinsa.