✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsayin sada zumunci a Musulunci 1

Ma’anar sada zumunci:  Sada zumunci shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da…

Ma’anar sada zumunci:  
Sada zumunci shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar ’yan uwa (ma’abuta zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gareb su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk bangarde ne na sada zumunci.
Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga dan uwa yayin haduwa da gaishe shi da ce masa yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi.
Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da rike amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a boye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunci ne.     
Hukuncin sada zumunci:
Wajibi ne Musulmi su sada zumuncin da ke tsakaninsu, kamar yadda shiryarwar Musuluci ta ginu kan haka, Allah Ta’ala Yana cewa: “Ka tuna lokacin da muka riki alkawari daga Banu Isra’ila cewa kada su bauta wa kowa sai Allah, kuma su kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci (’yan uwa) da marayu da miskinai, kuma ku gaya wa mutane kyakkyawan zance, kuma ku tsai da Sallah ku bada Zakka, sai kuka juya baya (ga barin wannan umarni), sai ’yan kadan ne daga cikinku, kuna masu bijirewa”
Kuma a suratul Bakara, aya ta 27 Allah Ya fassara fasikai a cikin fadinSa: “Su ne masu warware alkawarin Ubangiji (kan aiko Annabi SAW), bayan karfafa alkawarin gare su, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (zumunci), kuma suke barna a bayan kasa,wadannan su ne tababbu.”
Haka nan kuma a suratur- Ra’adi aya ta 21 Allah Ya bayyana ma’abuta hankali da cewa: “Kuma su ne masu sadar da abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (na zumunci), kuma suke jin tsoron Ubangijinsu, kuma suke jin tsoron mummunan hisabi.”
Haka Hadisai sun bayyana muhimmancin zumunci, kamar yadda Imam Bukhari da Muslim sun rawaito daga Sayyidina Jubairu dan Mud’im (R.A), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba.”
Ma’abuta zumuci:
Su ne duk makusantan mutum (na jini) na kusa ko na nesa, magadansa ne ko ba magada ba, muharramai ne ko ba muharramai ba, masu dangantaka da shi da suka hada da kakanni da iyaye da ’ya’ya da jikoki, ’yan uwa maza ko mata kanne da yayye da ’ya’yansu da ’yan uwan uba da na uwa.
Idan muka fadada ma’anar zumunci zuwa ga ’yan uwantakar Musulunci da bada hakki ga ma’abutansa, to kai-tsaye, aya ta 36 a Suratun-Nisa’i, za ta yi mana jagoranci ga raba ma’abuta hakkin kyautatawa zuwa gida uku, inda Allah Madaukaki Yake cewa: “Kuma ku bauta wa Allah, kada ku hada wani da shi a cikin bauta (shirka), kuma ku kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci da marayu da miskinai da makwabci ma’abucin zumunci da makwabci manisanci da aboki a gefe da dan tafarki da bayinku. Hakika Ubangiji ba Ya son wanda ya kasance mai takama, mai yawan alfahari.”
Bisa koyarwar wannan aya, za mu iya raba ma’abuta hakkin a kyautata musu zuwa gida uku:
a)    Mutum mai hakki uku: dan uwa na jini Musulmi kuma makwabci.
b)    Mautum mai hakki biyu: Musulmi kuma makwabci.
c)    Mutum mai hakki zaya: makwabci a gida ko a kasuwa ko abokin tafiya da ba Musulmi ba.
Falalar sada zumunci:
Falalar sada zumunci ba za ta kayyadu ba, sai dai kawai a faddi kadan daga ciki:
1. Tsawaitar rayuwa.
2. Wadatar zuciya.
3. Bunkasar dangi.
4. Tsallake Siradi cikin sauki.
5. Samun yardar Allah.
6. Samun hadin kai.
7. Samun shiga Aljanna da sauransu.
Kuma yawanci wadannan falalolin an ciro su ne daga Hadisan Annabi (SAW) kamar haka:
Hadisin Muslim daga Abu Huraira (RA) cewa, Annabi (SAW) a ce: “…Wanda ya kasance ya bada gaskiya da Allah da ranar Lahira, to ya sadar da zumuncinsa.” A wata ruwayar tasa kuma ya ce: “Wani mutum ya ce wa Annabi (SAW) ya Ma’aikin Allah, ina da makusanta, ina sadar musu zumunci, amma suna yanke min shi, ina kyautata musu suna munana min, ina yin afuwa gare su suna yi min wauta. Sai Ma’aiki (SAW) ya ce: “In dai ka kasance kamar yadda ka fada, kamar kana rabauta daga gare su ne bisa bakin zunubin da suke aikatawa ne, to, taimako daga Allah ba zai gushe ba a tare da kai a game da su, matukar ka dauwama kan hakan.”
A wata ruwayar Buhari daga Sayyidina Abu Huraira (RA), Ma’aiki (SAW) ya ce: “Ba mai sada zumunci ba ne, wanda in an je masa ya je, sai dai mai sada zumunci shi ne wanda in an yanke masa zumunci, sai ya sadar da shi.”     
Sayyidan Anas (RA) ya rawaito Ma’aiki (SAW) na cewa: “Wanda yake so a yalwata masa arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to ya sada zumuncinsa.” (Buhari da Muslim suka ruwaito). Har yau sun kara rawaitowa, daga Nana A’isha (RA) daga Ma’aiki (SAW) ya ce: “Zumunci na makale a jikin Al’arshi, yana cewa: “wanda ya sadar da ni, Allah Ya sadar da shi, wanda kuma ya yanke ni, Allah Ya yanke shi.”
Nana Asma’u ’yar Sayyidina Abubakar (RA) ta ce: “Mahaifiyata ta zo min, kuma mushrika ce a zamanin Ma’aiki (SAW), sai na tambaye shi cewa: “Mahaifiyata ta zo min kuma tana kwadayin wani abu a wurina, shin na iya sada zumuncinta?” Sai ya ce: “kwarai, ki sada zumuncin mahaifiyarki. (Buhari da Muslim suka ruwaito).
Har yau sun fitar  daga Abu Ayyuba Khalid dan Zaidin Al’ansari (RA) cewa wani mutum ya ce: “Ya Ma’aikin Allah (SAW), ba ni labarin aikin da zai shigar da ni Aljanna, ya nesanta ni daga wuta. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ka bauta wa Allah, kada ka yi shirka da shi, ka tsayar da Sallah ka bada Zakka, sannan ka sada zumunci.”

Ukubar yanke zumunta
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un,shi ne abin da za mu iya cewa, saboda abin da ya samu zumunci na balbalcewa, babu zumunci, dan uwa ya ga dan uwansa, kowa ya shige, saboda rashin sani, ko a kan sani. Ba a zumunci, mai kudi don girman kai da ganin sai dai shi a zo masa, talaka kuma don tsoron wulakanci, talaka da talaka kuma don tsoron kada ya dora wa dan uwansa nauyi.
Ayoyi da Hadisai da dama, sun ja kunne kan yanke zumunci. Ma’aiki (SAW) ya ce: “Mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba.” Buhari da Muslim daga Jubairu dan Mud’im.
Hanyoyin sada zumunci:
Ana sada zumunci ne ta hanyoyi da dama, kamar tattaki zuwa wurin ’yan uwa ko wasika ko wayar sadarwa ko sakon baka (a aika gare) ko shirya tarurrukan taya farin ciki ko jajanta wa wani.
Allah Ya inganta zumuncin da ke tsakanin Musulmi.

Habibu Muhammad Ayagi
Raudhatur-Rasul, Ayagi, Kano
07082460196
Imel: [email protected]