Kamar yadda aka sani, ranar 21 ga watan Maris, wato Ranar Rubutacciyar Waka ta Duniya, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin yin bitar matsayin rubutacciyar waka a jiya da yau da makomarta gobe.
Domin taya ’yan uwana marubuta da manazarta wakoki murnar zagayowar wannan rana, za mu yi nazari a kan matsayin rubutacciyar waka a adabin Hausa.
- Za A Fafata Yakin Basasa Muddin Aka Kashe Gwamnan Binuwe – Wike
- Ka’idojin Hadewa Da Kuma Rabe Kalmomi Yayin Rubutu
Bahaushe ya fara dandanar zakin rubutacciyar waka tun a wajen karni na 17.
A wannan karni an sami rubutattun wakoki kamar “Shi’ir Hausa” da “Jamuyah” dukkansu na Sheikh Ahmad Tila.
Sai Tarihi El-Sudan, ita ma waka ce ta Hausa da sunan Larabci ta Sheikh Abdulkadir Tafa.
Duk dai a karni na 17, an sami wakoki irin na su Wali dan Masani da Wali dan Marina a Katsina, da sauransu.
A karni na 18
A karni na 18, an ci gaba da samun marubuta wakoki irin su Malam Muhammadu bn Muhammadu al-Katsinawi wanda ya shahara a wajen shekarar 1732.
A karni na 18 zuwa na 19, an sami bunkasar marubuta wakoki irin su Malam Muhammadu na Birnin Gwari, 1758-1878, wanda yana daya daga cikin wadanda ake alakanta shahararriyar wakar nan ta “Gangar Wa’azu” zuwa gare su.
Sannan akwai shaihunnan malamai irin su Malam Shitu dan Abdurra’uf, mawallafin wakar “Jiddul Ajizi Ba’ajamiya”, da “Jimiyya”, d.s.
Haka nan akwai wakokin madahu na masu jihadi irin su Shaihu Usmanu dan Fodiyo da kaninsa Abdullahin Gwandu da dansa Muhammadu Bello, da Nana Asma’u da autansa Isan Kware, da sauransu.
Fitattun marubutan karni na 19
A karni na 19 zuwa na 20, an sami fitattun marubuta wakoki kamar su Sarkin Zazzau Alu dan Sidi, da (Dokta) Aliyu na Mangi da (Dokta) Akilu Aliyu da (Dokta) Alkali Bello Gidadawa da (Dokta) Mudi Sipikin, da Malam Ummarun Gwandu, da Malam Sa’adu Zungur a Bauchi, da Malam Mu’azu Hadeja da Abubakar Ladan Zariya da sauransu.
A sakamakon kwazo da nuna kishi na wadannan shaihunnan malamai, an sami habakar rubutacciyar waka a kasar Hausa.
Rubutacciyar waka a yau
A karni na 19-20, rubutacciyar waka na kamshin turare dan goma.
Bayan tumbatsar marubuta wakoki da aka samu, akwai litattafai da wallafe-wallafe da suka shafi rubutacciyar waka da dama.
Misali, wakokin “Imfiraji”, da “Fasaha Akiliyya”, da “Wakokin Mu’azu Hadeja”, da “Sababbi da Tsofaffin Wakokin Mudi Sipikin”, da “Baje Kolin Hajar Tunani” na Alkali Bello Gidadawa, da “Wakokin Sa’adu Zungur”, da “Wakokin Hausa”, da sauransu.
Koma-baya
Amma maimakon a karni na 21 a ce rubutun litattafai ya yi tashin gwauron zabo, sai aka sami ci gaban mai hakar rijiya.
Rubuce-rubuce sai suka koma a kafafen sada zumunta ko social media. Wannan ya kawo koma baya a fannin nazarin rubutacciyar waka.
Misali, a sakamakon dukufa wajen nazarin rubutattun wakokin magabatanmu, mun rabauta da samun farfesoshi a fannin rubutacciyar waka kamar su:
- Farfesa Dalhatu Muhammad
- Farfesa Dandatti Abdulkadir
- Farfesa Abdulkadir Dangambo
- Farfesa Bello Sa’id
- Farfesa Haruna Birniwa
- Farfesa A.B. Yahya
- Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa
- Farfesa Magaji Tsoho Yakawada
- Farfesa Bala Usman
- Farfesa Zulyadaini, da sauransu.
Kusan dukkan wadannan farfesoshi na fannin rubutacciyar waka za ka ga ayyukansu sun jibanci ayyukan marubuta wakoki ne mazan jiya.
Matsalolin rubutacciyar waka a yau
Zamani: A duk lokacin da wani abu ya yi tashin gwauron zabo, ana sa ran wata rana zai yo kasa.
Buga littattafai: Ta fannin buga littattafai, za ka iske kusan dukkan littattafan magabata, kamfanoni ne suka buga su. Da wuya ka ji wani marubucin waka ya buga littafinsa da kansa.
Akwai kamfanoni masu buga litattafai irin su NNPC da Gaskiya Corporation, da University Press da Alhuda-huda da Amana da Ahmadu Bello University Press, da sauransu.
A yanzu wadannan kamfanonin buga littattafai kusan in ce sun daina karbar littattafan da suka shafi rubutacciyar waka domin bugawa.
A wannan karni na 21, littattafan da suka jibinci rubutacciyar waka kalilan ne, masu su suka buga.
Misali, “Daurayar Gadon Fede Waka”, na Farfesa Abdulkadir Dangambo, da “Gadar Zare” na Dokta Awwal Anwar, da “Salo Asirin Waka” na Farfesa A.B Yahya, da “Bayanin Rubutacciyar Waka” na Farfesa Isa Mukhtar, da “Nazarin Waken Hausa” na Dokta Sulaiman A.S. Sarbi, da “Guzurin Marubucin Waka” na Malam Nasiru G.Ahmad ‘Yan Awaki”, sai “Matakan Nazarin Rubutacciyar Waka” na Malam Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya.
Rashin goyon baya
Wani abin da ke ci wa rubutun rubutacciyar waka tuwo a kwarya shi ne rashin goyon baya daga al’umma da hukumomi.
A da idan gwamnati na bukatar fadakarwa, ko wayar da kan jama’a a kan wani abu da ya shafi ci gaban al’umma, ana bukatar marubuta wakoki su ba da tasu gudummuwa wajen rubuta kasidu a kan batun da ake bukata.
A yanzu ba a yin haka. A yau in ka ga haka, sai dai yabo ga ‘yan siyasa.
A tarukan al’umma na cikin gari, a da a kan bukaci marubuta wakoki su baje kolinsu, wato su yi maraba da baki. A yanzu wannan ya yi karanci.
A Jami’o’i kuwa, a da dalibai na da zummar nazartar rubutacciyar waka. Amma a yanzu abin sai a hankali. Dalibai na guje mata saboda sun shaka cewa tana da wuya.
A jiya akwai gasa da Kungiyar Marubuta da Manazarta Rubutacciyar Waka ke shiryawa duk shekara.
A karshen gasar ana ba da kofi da sauran kyaututtuka ga zakarun. Wannan kan shajja’a mawaka wajen dagewa da inganta wakokinsu.
Ko da yake a yanzu akwai yunkuri da ake yi domin farfado da ayyukan da waccan kungiyar ke yi a karkashin Gamayyar Marubuta da Manazarta Rubutattun Wakokin Hausa ta Kasa, a bisa jagorancin Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya.
Yadda za a farfado da rubutacciyar waka
- Kamfunan buga littattafai su dawo da karbar littattafai na wakoki, ko a sami wani sabon kamfani na buga littattafan Hausa.
- Hukumomi su rika daukar dawainiyar buga littattafan Hausa masu ma’ana, kamar yadda ake yi a kasar Masar, da sauran kasashe. Wannan zai zaburar da marubuta wakoki.
- Jami’o’i da gwamnatoci su rika daukar dawainiyar shirya gasar rubutacciyar waka, ana ba da kyaututtuka ga zakarun gasar.
Alhamdulillah, a yanzu wajen shekara hudu zuwa biyar, ana ta yunkurin karfafa ko inganta rubutun kagaggun labarai.
Akwai cibiyoyi da ke daukar wannan, kamar BBC da Aliyu Gusau Library da Media Trust (masu wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya) da Dangiwa da Darma Library, da sauransu.
To a yanzu ya kamata a mayyazo zuwa ga rubutacciyar waka.
Kamar yadda aka sani ne, tubalan ginin adabin zamani uku ne: rubutacciyar waka, da rubutun zube, da wasan kwaikwayo.
Wadannan su ne tubala ko murahun adabin zamani. Idan ya kasance a kullum ana ta gina kafa daya daga cikin murahun, sauran biyun na zagwanyewa, ko an dora tukunyar ci-maka, ba za ta zauna ba, girkin zai tuntsure ya kashe wutar murhun.
Marubuta a hada kai
- Marubuta wakoki su dage su hada kansu. Makwabcinka, ko dan kwadigo, ba za su maka kaftu, da noma, da cirbe, da girbi, a gonarka ba kamar yadda za ka yi da kanka.
Godiya ga malaminmu Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda bisa jagorancinsa ne muke wannan tattaunawar.
Wata godiyar zuwa ga Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, bisa gasar rubutattun wakoki da suka shirya a kan tsaro.
Ba za mu manta da gwamnatin jihar Bauchi bisa karrama daya daga cikin magabatanmu, wato Malam Sa’adu Zungur ba, ta hanyar sauya sunan Jami’ar Jihar Bauchi zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur.
Mun tattauna da Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dokta Aliyu Tilde. Akwai shiri wanda suke yi na karrama marubuta wakoki a jihar Bauchi. Muna matukar godiya bisa wannan albishir.
Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya shi ne Shugaban Gamayyar Marubuta Da Manazarta Rubutacciyar Wakar Hausa ta Kasa.