Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne, (SAW).
Bayan haka, lallai mafi gaskiyar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), mafi kyawun shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu (Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkira a cikin addini, kuma duk abin da aka kirkira a cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya tsare mu daga gare ta, amin.
Sannan bayan haka, yau mukalar tamu za ta waiwaya ne zuwa daya daga cikin shika-shikan Musulunci, wanda lokacinsa ya karato, domin in Allah Ya so kuma Ya kai mu, ranar Juma’a mai zuwa muna cikin Ramadan, wanda azumtarsa wajibi ne da fadin Alkur’ani da Hadisi da haduwar malamai.
Matsayin azumtar watan Ramadan tilas ne ga duk wanda ya hada sharuddan yin sa. Za mu bayyana wasu al’amurran da suka shafi falala da hikimomin da ke tattare da azumin don kara fito da matsayin nasa. Muna fata Allah, cikin ikonSa da jinkanSa Ya sa mu dace da alheran da ke cikin watan da kuma gabatar da ibadojin da ke cikinsa a turbar ikhlasi. Amin!
Farko dai Alkur’ani yana cewa, “Ya ku wadanda suka yi imani, an wajabta muku azumi, kamar yadda aka wajabta wa wadanda suke kafin ku, tsammaninku, ko kwa samu takawa…. Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, kuma ayoyi bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa tsakanin karya da gaskiya, don haka dukkan wanda ya halarci watan a cikinku, to ya azumce shi. kuma wanda ya kasance mara lafiya, ko a kan wata tafiya to, (idan ya sha ruwa) sai ya rama a wasu kwanakin na daban. Allah Yana nufin sauki a gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani a gare ku. (An ce ku rama) don ku cika adadin (kwanakin Ramadan), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da Ya yi, kuma ku zamo masu godiya gare Shi.” Surar Bakara, aya ta 183-185.
Na biyu, Hadisai da yawa ingantattu, sun zo da bayanin wajibcin azumtar watan Ramadan. Misali kamar Hadisin dalhatu bin Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), cewa wani Balaraben kauye ya zo wa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ‘Ba ni labarin abin da Allah Ya faralta a kaina na azumi.’ Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Watan Ramadan, sai dai in kana son ka yi wani abu na tadawwa’i (ganin dama).” Buhari (46) da Muslim (11) ne suka ruwaito shi.
Sai kuma Hadisin Abdullahi bin Umar (Allah Ya yarda da su), wanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “An gina Musulunci a kan abubuwa biyar… (sai ya ambata) da azumin watan Ramadan….” Buhari (8) da Muslim (1151) suka ruwaito shi.
Na uku, Musulmi (haduwar malamai) gaba daya sun hadu a kan wajibcin azumtar watan Ramadan ta yadda duk wanda ya ji wani kaikayi a zuciyarsa kan haka ya kafirta. Allah Ya kiyashe mu da shakkar wani abu tabbatacce a addininmu, amin!
Daga cikin sharuddan azumi akwai mutum ya kasance lafiyayye, mazaunin gida, ya yi kuduri tabbatacce (niyya), wanda ya ayyana irin azumin da zai yi, kuma ya zama bayan faduwar rana, kafin fitowar alfijir; mace ta kasance cikin tsarki.
falala da hikimomin azumin watan Ramadan
1. Daga cikin falalar akwai bayanin da ya zo cewa Ramadan da Zul-Hajji tagwaye ne wajen cikarsu da kuma ladarsu da sakamakonsu ko da kowanensu ya yi kwanaki ashirin da tara-tara ne. Wato ba a rage musu komai daga cikin wannan matsayi, kamar yadda ya zo a Fatahul Bari, mujalladi na 4, shafi na 150; da Majmu’u mujalladi na 6, shafi na 253; da kuma Sahihu Ibnu Hibban, mujalladi na 8, shafi na 218 a littafin Ihsan.
2. Bayani ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda), cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Idan watan Ramadan ya shiga, sai a bude kofofin sama kuma a kulle kofofin Jahannama, a kukumce shaidanu.” Buhari (1899) da Muslim (1079) suka ruwaito shi.
3. Haka nan daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani (da wajibcin azumin) kuma mai neman lada (alhali ya yi don Allah kadai), an gafarta masa duk abin da ya gabatar na zunubinsa.” Buhari (38) da mujalladi na 4, hafi na157; da kuma Abu Hatim Ibnu Majah (1641) suka ruwaito shi. Abu Hatim Ibnu Majah ya ce, “Abin da ake nufi da ‘imanan’ shi ne yana mai imani da farillancin azumin; sannan ‘ihtisaban’ yana mai ikhlasi, mai tsarkake aikin saboda Allah kadai.”
4. Daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “(Tsakanin) Salloli Biyar (na farilla) da Juma’a zuwa Juma’a da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankarewar zunubbai ne da ke tsakankaninsu, matukar an nisanci kaba’irai (manyan zunubai).” Muslim (233) ne ya ruwaito shi.
5. Cikin watan Ramadan akwai kwanaki goma na karshe da suke da matsayi babba, musamman da yake ana riskar Daren Daraja (Lailatul kadri), wanda shi kansa yana da falala ta musamman, idan hali ya samu nan gaba za a gabatar da bayani kansa, in Allah Ya so.
6. Azumin Ramadan yana daya daga cikin mafi girman ayyukan biyayya ga Allah Mahaliccin kowa da komai. Hasali ma dai wani sirri ne tsakanin bawa da Mahaliccinsa, kuma wata kaiwa matuka ce ta cikar amana.
7. Wani al’amari ne na falalar hakuri, musamman da yake nau’uka uku na hakuri sun tattaru a kansa: Hakuri a kan biyayya ga Allah da hakuri a kan kin saba wa Allah da hakuri a kan abin da Allah Ya sanya na radadin kaddararSa.
8. dandanar tsarin rayuwa na girman abubuwan da aka girmama na haramci da yunwa. Abin da ke sa bawa ya tuna ni’imar Allah gare shi wadda ta doge, sai ya tuna ’yan uwansa fakirai (matalauta), wadanda suke cikin wannan lamari na rashi duk tsawon shekarar ma.
9. A cikin azumi akwai fa’idoji na lafiyar jiki, domin azumi wani hutu ne na wasu sassan jiki daga aikace-aikacen da suke yi na tace abinci da rarraba wasu abubuwa nan da can, ta yadda da yawa akan samu nishadi da karfin zuciya, musamman da yake an takura wa Shaidan gudana cikin jini ta yadda tu’anntin da yake yi kan ragu.
10. Shi azumi ibada ne ‘jalilah’ (mai daraja), wanda ya tattara sassan alheri gaba daya kuma ya nisantar da sassan sharri gaba daya, tun ma dai ba in aka dubi abin da ake samu ba na takawa, wadda yake sa a ji tsoron Allah Madaukaki; a yi aiki da abin da aka saukar na Alkur’ani; a hakura da kadan (abin da Allah Ya bayar na arziki); sannan a yi hankoron tattalin abin da za a tafi shi Lahira. Allah Ya mu dace!!
Wassalaamu alaikum warahmatullah!