✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolinmu sun samo asali ne daga mulkin mallaka — Obasanjo

Tsohon shugaban ya ce akwai alaka tsakanin tattalin arziki da sauya tsarin siyasa a Najeriya.

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce wasu daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta sun samo asali ne tun daga lokacin turawan mulkin mallaka. 

Obasanjo, ya bayyana haka ne yayin gabatar da wata maƙalar littafi a ranar Asabar a Enugu.

“Duk tsarin da aka gabatar na tattalin arziki matukar babu gwamnatin mai manufa ga kuma gurgun tsari da ake fama da shi, wadannan abubuwan sai sun durkusar da tsarin.

“A matsayinmu na kasa, tarihinmu a bayyane yake mun sha fama da matsaloli a baya, kuma mun yi rashin damarmaki muhimmai,” in ji.

Tsohon shugaban ya ce akwai alaka tsakanin tattalin arziki da sauya tsarin siyasa a Najeriya.

Ya ce tarihin yadda aka samar da kundin tsarin mulkin Najeriya da tubalin da aka dora siyasar kasar sun nuna akwai wani gurbi da aka bari, wanda yake bukatar a cike shi.

A cewar Obasanjo akwai bukatar dora tubalin kasar nan a kan gwadabe mai tsari da zai yi daidai da mutanenta.

Kazalika, ya ce matuka ba samu jajirtattun shugabanni da za su tabbatar da tsarin da ya dace da kuma cike gibin matsalolin da Najeriya ta gada tun turawan mulkin mallaka, abu ne mai wuya a samu sauyin da ake muradi.