Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. In sha Allah za mu karasa bayanin magance mugunyar gajiya don dawo da sha’awar da ta dauke, da fatan wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Matakan Dawo Da Sha’awa
Maganin Mugunyar Gajiya:
Ga uwargidan da ta fahimci cewa daukewar sha’awarta tana da nasaba da tsanin gajiya kamar yadda bayaninta ya gabata a makon jiya, sai ta bi wadannan hanyoyin don magance mugunyar gajiyar nan, wanda yin hakan zai yi sanadiyyar dawowar sha’awarta cikin yardar Allah.
Fahimta Kyakkyawa:
Mafi kyawun hanyar magance kowace irin matsala shi ne yi mata kyakkyawa kuma cikakkiyar fahimta, da haka ne za a iya samun nasarar maganceta.Amma idan babu fahimta mai kyau to yin maganinta zai zama mai wuya ko kuma garin neman maganin ya zama sanadiyyar karuwarta ko bullowar wata matsalar daban. Don haka yana da matukar alfanu ga uwargida ta fahimci wannan matsala ta mugunyar gajiya da dangantakarta da halayya da cikakkiyar fahimta. Ta fahimci abubuwan da suke bayyanar mata da mugunyar gajiya da kuma abubuwan da mugunyar gajiya take haifar mata yayin da ta bayyana a gare ta.
Ita mugunyar gajiya matukar ta taru a cikin ma’aikatar hankali to dole sai ta samu hanyar fita ta halayya, da kuma mu’amala, watau za ta bayyana ta hanyar yadda mutum yake mu’amulantar al’amuran da suke faruwa a cikin rayuwa ta yau da kullum.
Abubuwan suke tsokano mugunyar gajiya har ta bayyana a cikin halayya da mu’amula sun kasu gida uku:
(1)Manyan Fitintinu na rayuwa irin wadanda Allah ya ke jarraba wani mutum ko al’umma duka da ita; kamar gobara, ambaliyar ruwan sama, yaki da sauransu; wannan yana saka mutane da yawa cikin tsananin kunci da ke haifar masu da mugunyar gajiyar mai tsananin tasiri cikin al’amuransu na yau da kullum.
(2) Mummunar kaddara ko wata masifa da ta fado wa mutum cikin rayuwa, kamar rasuwar wani daga cikin makusantan mutum miji ko mata, da ko iyaye; mutuwar aure, tsananin talauci, rashin aikin yi, rashin lafiya, da sauransu.
(3) Matsalolin rayuwa na yau da kullum kamar damuwa game da kula da yara da tarbiyyarsu, kula da gida, rashin samun biyan wasu bukatu na rayuwa, rashin kyakkyawar danganta da jama’a, sabawa da mafi kusanci ga mutum daga mutane, da sauransu.
Faruwar ire-iren wadannan abubuwa da ke sama yana sanya bakaken shau’uka su bayyana cikin zuciya kuma su yi tasiri a cikin ma’aikatar hankali da haka har su juyar da dabi’u da tsanantar al’amuran cikin rayuwa. Irin wadannan bakaken dabi’u sun hada da yawan fargaba, kunci da bacin rai da bakin ciki da yawan jin haushi, munana zato da sauransu. Wadanda idan aka bar su suka dade a cikin zuciya sai su haifar da yamutsi a cikin zuciya da rashin walwala da sakewa, a hankali sai su saka mutum a cikin tsananin bakin ciki kuma su raunata yadda yake ma’amulantar mutane da sauran al’amuran rayuwa na yau da kullum.
Don haka duk matar da ta zama mai yawan fada da mijinta da jin haushinsa, alhali da ba haka take ba, da matar da take jinta kullum zuciyar ta a yamutse ta kasa samun walwala, da sauran ire-iren haka alama ce ta cewa suna cikin tsananin lahani na mugunyar gajiya.
Don haka sai uwargida ta auna ta gani don tantacewa ko tana cikin halin mugunyar gajiya, ta hanyar yin la’akari da dabi’un da suka fi yawan kai wa da komowa a cikin zuciyarta da kuma la’akari da yadda take mu’amula da mijinta da ‘ya’yanta da makwabta da ‘yan’uwa da sauransu. Idan uwargida ta tabbatar cewa tana cikin lahanin mugunyar gajiya sai ta bi wadannan hanyoyin don magance ta, wanda yin hakan shi ne zai dawo mata da sha’awarta.
Makarin Mugunyar Gajiya:
Makari na Farko shi ne yakar mugunyar sha’awa take yanke da faruwarta, kar a bari ta dade har ta bi jiki ta zama dabi’a.Yin hakan shi zai jefa mutum cikin yawan kunci da tsananin bakin ciki. Hanyoyin yakar ta shi ne ta hanyar tunkude duk wata bakar dabi’a da ta bayyana a cikin zuciya da maye gurbinta da kyakkyawar dabi’a. Misali, take yanke sai a maye gurbin fargabar faruwar wani mummunan abu da kyakykyawan tunanin yin tawakkali ga Allah da mayar da dukkan al’amura gare shi. A maye gurbin tsoro da amincewa da zuwan kariya da taimako daga Allah, sannan a maye gurbin dukkan mummunan zato da kyakkyawan zato. Bayan haka sai a aiwatar da ayyukan da za su fitar da mutum daga kangi da halin kaka ni kayin da mugunyar gajiya ta saka shi; misali ga matar da take fama da tsananin mugunyar gajiya saboda ayyukan kula da gida da yara da suka cakude mata, sai ta yi kokarin tsara lokuta da ayyukan da yin kowane aiki cikin farkon lokacinsa kuma bisa ka’idarsa ba tare da yin jinkiri ba. Idan ta dage tana bin haka sawu da kafa za ta samu sauki da gushewar mugunyar gajiyarsa ta dauke mata sha’awa.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance a cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.