✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolin kunne da hanci da makoshi

Likita tun da ka yi bayanin cututtukan idanu, muna so ka yi bayani kuma a kan cututtukan kunne, tun da na san wasu da dama…

Likita tun da ka yi bayanin cututtukan idanu, muna so ka yi bayani kuma a kan cututtukan kunne, tun da na san wasu da dama suna da matsalar, ciki har da ni.
Daga Ibrahim, Gusau da Mujahid, Hadeja
Amsa: Su matsalolin kunne ba yawa ne da su ba, shi ya sa ma a likitance ba a dauki kunne shi kadai aka yi masa fanninsa daban ba, sai aka hada shi da hanci da makogwaro. Wato likitocin kunne ba kunne kawai suke dubawa ba, har da hanci da makoshi.
Kunne: Shi kunne amfaninsa ji da sa mana daidaito idan mun mike tsaye. Don haka idan ya samu matsala, akan iya samun ciwo, raguwar ji, ko jiri. Kunne an kasa shi zuwa bari; wajen kunne, tsakiyar kunne, da cikin kunne. Da fatar kunne da bututun kunne su ne waje, daga marfin kunne zuwa kasusuwan kunne su ne tsakiya, wanda ya hada har ila yau da kofar da ta tafi makogwaro, can cikin kunne kuma akwai jijiyoyin jini da na laka da dodon kunne.
Cututtukan da suka fi addabar kunne su ne na shigar kwayoyin cuta da kuma kurumta. A wasu lokuta wasu abubuwa kamar wake, kwari da abubuwan wasan yara sukan shiga kunne ta yadda dole sai an je asibiti an cire.
Shigar kwayoyin Cuta: kwayoyin cuta ba inda ba za su iya shiga ba a jikin dan Adam, ciki har da kunne. Duk da cewa kwayoyin kan shiga cikin kunnen kowa manya da yara, matsalar ta fi yi wa yara lahani. Alamunsa sun hada da fitar da ruwa ta kunne, wani lokaci mai miki, ciwon kunne (yawan kuka da jan kunne a yara) da zazzabi. Yawanci kwayoyin ta makogaro suke shiga tsakiyar kunne, tun da mun ce akwai hanyar da ta hada su, kafin su shiga ciki. Don haka yaro sai ya fara mura da tari a mafi yawan lokuta kafin ya yi ciwon kunne. Idan kuma aka ga fatar kunne ta yi ja, ba mura ba tari to ta fatar kunne suka shiga.
kwayoyin cuta iri-iri kamar na sankarau da kyanda su kuma sukan iya shiga can cikin kunne. Yawanci duk abin da ya taba can cikin kunnen zai iya kawo kurumta.
Kurumta: Za ta iya faruwa ta sanadiyyar abubuwa da dama, kamar shigar kwayoyin cutar sankarau ko shan wasu magunguna (irinsu kuinine na zazzabin cizon sauro) da sukan lahanta abubuwan da ke can cikin kunnen. Wadannan abubuwa biyu, wato sankarau da magunguna su suka fi kawo mana kurumta. Wasu ’yan kadan kuma haka nan aka haife su. A manya masu ji, hadari na buguwa a kunne ko yawan shekaru ko aiki a wuri mai kara ko shigar wani sinadari na kyamikal cikin kunne, duk sukan iya sa raguwar ji ko ma kurumta. Wasu za a iya gyarawa wasu kuma ba magani. A iya tuntubar babban asibitin bangaren kunne don a bincika.
Hanci: Amfanin hanci sun hada da shakar iska zuwa huhu da tace ta daga kwayoyin cututtuka da dumama ta ta hanyar wasu ramuka a saman hancin. Sai kuma jin kamshi ko wari. Cututtukan hanci ba su wuce na mura da fitowar tsuro ba. Su habo da zubar ruwa daga hanci duk alamu ne na wata matsala ko a hanci ko a jini ko a kwakwalwa, ba matsaloli ba ne a kan kansu na hanci kawai. Wato yana da kyau a gane bambancin cuta da alamomin cuta, don ba daya suke ba.
Mura: Kan iya addabar kowa manya da yara, maza da mata. Akwai wadda kwayoyin cuta na birus suke kawowa, akwai kuma wadda abubuwan da ke cikin iska suke kawo wa wasu, kamar burbushin kura ko na karmami ko na gashin mage ko na gashin darduma da dai sauran ire-irensu. Murar kwayoyin cuta takan sa zubar hanci, toshewar hanci, atishawa da dan zazzabi ko ciwon kai kuma da kanta take tafiya ko ba a sha magani ba. Yawanci kwayoyin cutar sun fi yawa da bazaar, shi ya sa aka fi yi a lokacin. Kuma duk mai ita idan ya yi atishawa sai ya saki miliyoyin kwayoyin a iska, idan wani na kusa da shi ya kwasa
Murar kwayoyin cikin iska ta fi zafi (a alamunta akwai kaikayi da toshewar hanci amma yawanci ba zubar ruwa), kuma takan yawan dawo wa masu ita duk lokacin da mutum ya shaki abin da hancinsa ba ya so. Shi yake sa wasu suke tambayar mura da ta ki tafiya kuma ta ki jin magani. Idan ba a yi maganin abin a cikin iska ba, ba ta tafiya. Misali, mai murar kurar darduma sai ya cire darduma a gidansa zai samu sauki, mai murar dussar karmami, sai ya rufe hancinsa idan za shi gona, mai murar gashin kyanwa sai ya dauke kyanwa a gidansa. Wato dole ne dai mai irin wannan mura sai ya gano abin da yake ba shi murar, ba likita ne zai gano masa ba. Wannan ciwo kanin ciwon asma ne.
Tsuro a hanci: Akan samu a kan hanci (yawanci a fararen fata) ko a cikin hancin. Na cikin hancin ya fi fitowa masu muguwar mura irin ta abubuwan cikin iska. Alamunta sun hada da toshewar hanci da kaikayin hanci, idan wani ya leka ma zai iya ganinsa da ido. Ba ya zama kansa, da an yanke a asibiti shi ke nan. Amma zai iya dawowa.
Makoshi: Amfaninsa shi ne hada hanci da huhu da kuma hada baki da makogwaro. Sai kuma kama kwayoyin cuta na iska da kashe su don kada su shiga huhu, ta hanyar wadansu halittu guda uku a bangonsa da ake kira ’yar wuya. A wasu lokuta kwayoyin cutar da ’yar wuyar ta kama kan yi yawa, su sa kumburi da ciwo ko kaikayi da tari har sai an ba mutum magani. Kayan yaji da kayan kanshi na abinci sukan iya taimaka wa makoshi wajen wannan aiki amma a hannu daya kuma sukan iya sa gyambon ciki.
daya ciwon da kan iya kama makoshi shi ne tsuro mai zama daji. Ta fi kama masu zukar taba sigari da barasa da burkutu. Sai dai an fi gani a fararen fata fiye da bakake. Alamomin su ne dusashewar murya, numfashi mai kara da wari, ciwon wuya da yawan tari.

 

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin Tambayoyi

Me ke kawo mutuwar jarirai a ciki tun kafin a haifo su?
Daga Sani B. Mubi
Amsa: Idan ka ce mutuwar jariri a ciki kana nufin mutuwar jariri a ciki bayan ya cika wata shida, domin akwai bambanci da kbari wanda ke nufin mutuwar jarirai a ciki kafin watanni shida kuma akwai bambancin sanadi. Abubuwan da suke kawo naka ba su wuce cututtuka a jikin uwa ba ko kuma abin da ke cikin. Na jikin uwa su ne shigar kwayoyin cuta mahaifa ta jini, kamar kwayar kanjamau, zazzakbin cizon sauro, sai hawan jini irin mai tsananin nan mai kawo jijjiga, shi ma yakan halaka abin da ke ciki, sai ciwon suga da shan barasa da buguwa a ciki yayin hadari ko duka a ciki irin na mai gida yayin wata rashin jituwa, wadda kan iya tsinka cibiya.
A jaririn kuma matsalolin kammaluwar halittu idan uwar ba ta sha magungunan da suka kamata ba kan iya sa a rasa jaririn. Sai kuma yawan abin da ke ciki. Sau da yawa tagwaye ko fiye, akan haifi wani da rai wani ba rai, domin wani kan shanye wani.
Akan iya kuma samun akasin launi ko kalar jini na rukunin Rhesus (wanda akan ba alamun ‘+’ da  ‘–‘) ba na ABO ba. Idan yaro + ne uwar – to akwai matsala. Idan cikin fari ne yawanci jariri na rayuwa amma duk wadanda za su zo bayansa ba su kai labari idan ba a gano da wuri ba an yi sauri an yi wa uwar allurar Rho-Gam ba a asibiti. Wannan na daya daga cikin manyan abubuwan da kan kawo mutuwar jarirai ga mata marasa zuwa awo. Da yawa za ka ji an ce “wance haihuwarta daya kawai, sauran duk a ciki suke mutuwa.” To yawanci matsalar ba ta wuce wannan.
Akwai bambancin wannan da wadda ba ta takba haihuwa ba amma tana yawan kbari. Wannan yawanci ba ya wuce matsalar mahaifa ba, wadda ba ta iya rike dan tayi; wadda kuma ba ta ma takba daukar cikin ba ma daban.
Daga shekaru nawa mace ke daina haihuwa?
Daga Maman Al’amin, Kano.
Amsa: Tsakanin shekaru na 45 zuwa 55 ake samun haka, wato zai iya faruwa a kowace shekara a wannan tsakani, don wasu sai a 46, wasu sai 52 da sauransu. Ba haihuwa ba ma har al’ada za ta tsaya cik. Mace za ta ji alamu iri-iri kamar yawan zufa, rashin barci, yawan gajiya da sauransu. Wasu sukan ji wasu abubuwan daban.
Sai yaro ya shekara nawa ake so a daina ba shi nono?
Daga Usman Bala, Ningi
Amsa: Ko da an fara ba yaro kamu da dan abinci daga wata na shida, ya kamata a ci gaba da shayarwa shekara daya har zuwa biyu. An fi so dai a cika biyun amma ya danganta da yawan ruwan nono da lafiyar uwar da yawan jariran (da yawa masu tagwaye ko fiye ba sa iya wuce shekara daya suna shayarwa).