Sakamakon yawaitar hatsarin jiragen sojin Najeriya a ’yan shekarun nan, Aminiya ta gano matsalolin da ke tattare da jirgin da ya yi hatsari a Kaduna ya kashe matukansa a baya-bayan nan.
Guruf Kyaftin Sadiq Garba Shehu mai ritaya, tsohon matukin jirgin soja ne, ya shaida wa Aminiya cewa bisa alkaluman da ake da su, yawan hatsarin riragen ya kai a iya cewa kusan duk bayan wata uku ake samun hatsarin jirgin soja a Najeriya.
- Maniyyata Aikin Hajji sun yi zanga-zanga kan ninka kudin kujera
- Aike wa Ukraine makamai: Amurka na kokarin tsokano tsuliyar dodo – Rasha
Hakan, a cewarsa, “Ya nuna cewa akwai wasu abubuwa da ba ma yi kuma dole ita Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yi nazari a kansu,” duk da cewa akwai abubuwa da yawa da ke kawo hatsarin jirgi.
Matsalolin jirgin da ya fadi a Kaduna
Da yake magana kan jirgin sojan da ya yi hatsari a Kaduna ya kashe duk matuksansa biyu, Guruf Kyaftin Sadiq, wanda masanin harkokin tsaro da aikin soja kuma mai bincike da ba da shawara ne, ya ce jirgin ba shi da laimar da matuki zai sauka idan ya samu matsala.
“Ba tare da tayar da hankalin jama’a ba, idan ka duba tarihin shi wannan jirgi da ake kira Mushak, jirgi ne mai yawan yin hatsari.”
Saboda da yawan tarihin hatsarin jirgin na Mushak, kirar kasar Pakistan, masanin ya ce, “In ni ne zan saye jirgi, wannan jirgin, kamar yadda na fada, game da abin da na sani a kansa, ba ma jirgin da za a saya ba ne”.
Tsohon hafsan sojin saman ya ci gaba da cewa “Wannan jirgi na Mushak, tun da aka yi shi a shekarar 2003 ya yi hatsari sau 31.
“To a gaskiya idan ni mai sayen jirgi ne ko mai bai wa gwamnati shawara ne, wannan jirgin tun farko ma ba zan neme shi ba.”
A rundunonin sojin duniya, a cewarsa, biyar daga cikinsu ne kawai suke amfani da Mushak, wanda “Wannan babbar aya ne da zai nuna wa wanda zai sayi jirgi cewa kada ya sayi wannan jirgi.”
Masanin ya kara da cewa babbar aya ce a ce duk yawan rundunonin sojin duniya, guda biyar ne kawai suka sayi wani jirgi.
Abubuwan da ke kawo hatsarin jirgi
Da ya juya kan abubuwan da ke kawo hatsarin jiragen sama, Guruf Kyaftin Sadiq, ya ca sun kasu gida uku: Kuskuren dan Adam, da na’urar jirgi, da kuma ikon Allah.
Ya bayyan cewa, “Kashi 80 cikin 100 na hatsarin jirgi a ko’ina a duniya, za ka ga shi mai tukin ne ya yi wani kuskure, sauran kashi 15 kuma za a iya sa wa a kan shi jirgin.”
Ragowar kashi biyar kuma abu ne da Allah Ke kawowa wanda ya fi karfin mutum da jirgin, “Kamar wani abu da Allah Ya kawo na yanayi” ko iftila’i.
Hatsarin jiragen sojin Najeriya
Da yake karin haske kan musabbabin hatsarin jiragen sojin Najeriya kuma, masanin ya ce zargi rashin yin abin da ya kamata daga bangaren gwamanti da kuma Rundunar Sojin Najeriya su ne uwa uba.
Tsohon matukin jirgin sojin ya ce akwai gazawar shugabannin siyasa wajen fahimtar yadda za su gudanar da aikin soji.
“Sun kasa samun horo kan yadda za su duba aikin soja; Ba su da shi (horon) kuma ba sa neman masana su yi musu bayani a kan sha’anin aikin soja.
“Saboda rashin wannan kwarewar, duk abin da sojan kasa ko sojan sama ko sojan ruwa suka kawo musu, kawai sa hannu suke yi.”
Ya ce lamarin tsaro, “Ba bayar da kudi ba ne kawai, dole in ka bayar da kudi ka tabbatar me ake saya.”
Magance hatsarin jiragen soji
Ya bayyana cewa daga cikin yadda za a magance hatsarin jiragen sojin akwai tabbatar da kwarewar matuka da ba su horo tare da bibiyar tarihin duk nau’in jirgin da za a saya.
A cewarsa, wajibi ne Rundunar Sojin Saman Najeriya ta mayar da hankali wajen horas da matuka jirginta a-akai-a-kai.
“A tabbatar da cewa a koyaushe matuka jirginmu suna hawa jirgi, saboda ya zama hannunsu ya kware.
“Inda hatsarin yake ke nan, saboda duk lokacin da matukin jirgi ya dade bai hau ba, to ranar da ya hau akwai wasu abubuwa da zai manta, akwai wata tangarda da za a samu.”
Abu na biyu shi ne tarihin jirgin, wanda ya ce abu ne da ya kamata gwamnati ta ba wa muhimmanci.
“Idan jirgi ya yi hatsari, abin da mu masu bincike ke fara dubawa shi ne tarihin wannan jirgin, ko ba a Najeriya ba —jirgi ne mai yawan hatsari?”
Sannan, “Idan ka ga rundunonin soja da yawa ba sa sayen wani jirgi, to hakan ya nuna cewa jirgin yana da matsala.
“Shi Mushak idan ka duba, har a yanzu ina ji kasashen da suka saye shi suna amfani da shi ba su fi biyar ba.”
Ya kara da cewa babbar aya ce a ce duk yawan rundunonin sojin duniya, guda biyar ne kawai suka sayi wani jirgi.
Asarar hatsarin jirgin soja
Asara ce babba ake tafkawa idan jirgin soja ya yi hatsari, baya ga ran da aka rasa, wanda shi ba za a iya kimantawa da kudi ko mayarwa ba.
Akawai kuma yi asarar kwarewa, “Su wadanda suka rasu a baya-bayan nan, ba matuka ba ne kawai, masu koyar da tukin jirgi ne; Wannan shi ma wani mataki ne, don ba kowane matukin jirgi ke iya koyarwa ba.”
Ita kanta rundunar martabarta na raguwa a idon duniya, “Saboda kowa ana gwada shi – Duk rundunar da take yawan samun hatsari haka, to martabarta raguwa yake yi”.
Ga kuma asarar makudan kudade, saboda “Horon matukin jirgi yana cin kudi sosai; Da farko sai ya yi awa 150 yana tuka jirgi a sararin samaniya a Kaduna.
“Daga na za a kai shi Kano, bayan ya kammala, idan ji jirgi mai saukar ungulu ne a kai ka Fatakwal ko Inugu ya je ya yi; idan jirgi mai mikakken fukafiki me za a kai ka Kainji.
“Idan aka duba kudin jirgin da kudin mai — wanda ka horas awa zai yi da jirgi a sama, man nawa ya kona, kudaden da aka kashe wajen kai shi horo a kasar waje, banda ran dan Adam wanda shi ba za a ka iya mayar da shi ba.”
Maganin matsalar
Da yake magana kan yadda za a magance yawan hatsarin jiragen sojin, ya ce, Rundunar Sojin Saman Najeriya ta mayar da hankali wajen horas da matuka jirginta a-akai-a-kai.
Ya ce idan matukin ya dade bai hau jirgi ba, hakan na iya kawo matsala, “Abin da za a yi shi ne a tabbbatar da cewa a koyaushe matuka jirginmu suna hawa jirgi, saboda ya zama hannunsu ya kware;
“Inda hatsarin yake ke nan, duk lokacin da matukin jirgi ya dade bai hau ba, to ranar da ya hau akwai wasu abubuwa da zai manta, akwai wata tangarda da za a samu.”
Abu na biyu shi ne bibiyar tarihin jirgin da za a saya, “Idan ka ga rundunonin soja da yawa ba sa sayen wani jirgi, to hakan ya nuna jirgin yana da matsala.”
Na uku, tabbatar da cewa jirgi yana da abubuwan da ya kamata na ceton rayuwa, kamar laimar sauka da sauransu.
Gurguwar dabara ce sayen jirgin da idan wani ya samu matsala matukinsa babu abin da zai iya yi, a cewarsa.
Ya ba da misali cewa a shekarun baya, jirgin da yake tukawa ya taba samun matsala a sararin samaniya, “Da irin wannan laimar na fita.”
Sai dai ya ce jirgin Mushak da ya yi hatsari a Kaduna na koyo ne, duk da cewa matukansa da hatsarin ya ritsa da su kwararru ne, amma babu laimar sauka.
“Jirgin da ake amfani da shi wajen koyarwa, akwai abubuwan da ya kamata yana da su; alal misali, jirgin ba shi da irin laimar fita idan matuki yana cikin hatsari,” inji shi.
Abin da ya kamata a yi
Guruf Kyaftin Sadiq ya ce wajibi ne shugabannin siyasa su zama masu kware kan yadda za su binciki aikin soja sannan su rika bibiya.
“Ba bayar kudi ba ne kawai, dole idan ka bayar da kudi ka tabbatar me ake saye, wannan jirgin mene ne tarihinsa? In ba haka ba, kana zuba ruwa ne a cikin kwando,” inji shi.
Abu na biyu shi ne su rika yin bincike kan duk abin da maganarsa ta taso domin kar su bari a yi zaben tumun dare.
Ya kara da cewa kamata ya yi duk sojan da zai gabatar da wani abu a gaban majalisa, su kuma “Kafin ya zo sun yi bincike.
“Kamar yadda muke maganar Mushak din nan, ya kamata Kwamitin Sojan Sama, lokacin da aka ce za a sayi wannan jirgin, nan da nan wani zai ce, ‘Ba wanan Mushak din ba ne ya yi hatsari a Pakistan? Ba za mu saye shi ba’.
“Amma maganar gaskiya mutum nawa ke da wannan ilimin, sau nawa kika ji an yi hakan?”
Ya ce duk da cewa sojojin na da laifi, “Amma kashi 80 cikin 100 laifin wanda zai sa hannu a fitar da kudaden ne, saboda soja tambaya yake yi,” kuma a kwarkashin gwamanti yake yi.
Da ya waiwayi sojojin ya bayyana cewa, “Wani lokaci sojojin ba sa fada wa ‘yan siyasa gaskiya.
Ya kamata idan sojoi sun ce sun son wani abu, ya kamata ’yan siyasa su bincika su tarihi da ingancin abin, wanda rashin haka ke jawo asarar rayuka da dukiyar gwamnati.