Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana takaddamar da take tsakaninsa da gwamna mai ci, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.
Bafarwa ya fayyace takaddamar ce a wurin taron masu ruwa-da-tsaki na Jam’iyyar PDP da aka gudanar a Asabar da ta gabata, kamar yadda wakilinmu ya samu bayani bayan gama zaman da aka yi a asirce.
- Za a kebe wa mutanen da ba Umrah suke ba lokacin sumbatar Hajarul Aswad
- An kashe malami da dalibi a wata Kwaleji a Legas
Alhaji Bafarawa ya ce yana godiya ga Gwamna Tambuwal da ya yarda su hadu, don hakan na iya sa kwalliya ta biya kudin sabulu.
“Ana son sanin mene ne gwamnati take ciki, shi kuma shugaba yana son sanin halin da mutanen suke ciki,” inji Bafarawa.
Ya kawo wani misali kan abin da ya faru a tsakaninsa da tsohon Shugaban Kasa marigayi Alhaji Shehu Shagari (Allah Ya gafarta masa), ya ce wata rana ya je ofishina ya ce Gwamna kana aiki.
“Amma akwai mutum biyu, ka saurari daya kada ka saurari dayan.
“Duk wanda yake yabonka ya ce kana aiki kada ka saurare shi, amma ka saurari wanda zai soke ka in sukar tana da amfani, domin shi ne masoyinka.
“Mai yabonka zai kashe maka jiki, ba ka gane wannan sai ka bar kujera, aikinka zai sa a tuna da kai kuma ina fata Mai girma Gwamna zai dauki wannan.
“A yanzu duk abin da za ka yi ba za a yaba ba, ba za a gode ba, sai ka bar kujerar,” inji Bafarawa.
Ya ce “Gwamna abin da ke damunmu da halinka shi ne boye bayanai ga talakawa, don muna ganin ana kwararmu.
“Lokacin da na bar ofis ban boye komai ba, kuma na bar kudi. Kai ka zo ka gaji bashi, ko kana so ko ba ka so, sai mun matsa mun san yadda gwamnatin da ta gabata ta kashe kudadenmu.
“Gwamnatin Jihar Sakkwato ba ta mutum daya ba ce, duk tamu ce amma dole akwai Shugaba,” inji Bafarawa.
Ya roki Gwamna Tambuwal ya kula da malamai domin in malamai na addu’a Allah zai kawo sauki, don haka akwai bukatar yin kwamitin malamai ’yan siyasa magoya bayan Jam’iyyar PDP.