Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Gumi, ya gana da tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo a Jihar Ogun.
Tawagar malamin ta isa harabar dakin karatu na tsohon shugaban kasar da ke birnin Abeokuta da misalin karfe 11.00 na safiyar Lahadi.
- Bollywood: Akshay Kumar ya kamu da COVID-19
- Mutum 44 sun mutu bayan ambaliyar ruwan da girgizar kasa ta jawo a Indonesia
Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Kehinde Akinyemi ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan wanda a cewarsa tawagar ta kunshi wasu jagorori na addini.
“Tabbas Gumi da wasu shugabannin addinai sun gana da Baba,” a cewar Akinyemi.
A bayan nan shehin malamin ya rika ganawa da wasu kungiyoyin ’yan daban daji a jihohin Zamfara da Neja inda yake tattaunawa da su a kan sakin mutanen da suka fada hannunsu a matsayin garkuwa.
Kazalika, Shehin Malamin ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta yi sulhu da ’yan bindigar da suka rungumi zaman lafiya ta hanyar ajiye makamai.