Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya yaba wa al’ummar Zariya kan jajircewarsu wajen kare kai daga bata-gari.
Ya bayyana satar mutane don neman kudin fansa da wasu ke yi da cewa abar la’anta ce.
- Sojoji sun ragargaji ’yan Boko Haram a Gwoza
- Yadda aka yi jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano
- Yadda mutanen gari suka kama ’yan bindiga a Zariya
Sarkin Zazzau ya bayyana haka ne a fadarsa da ke birnin Zariya ranar Litinin.
Kalaman nashi na zuwa ne bayan wasu al’ummar gari sun yi kukan kura suka cafke wasu ’yan bindiga biyu da suka shiga Zariya domin satar mutane ranar Lahadi.
Aminiya ta rawaito cewa wasu ’yan bindiga biyu ne dai suka shiga rukunin gidaje masu saukin kudi da ke Kofar Gayan a Zariya a ranar Lahadi, inda suka yi yunkurin sace matan aure biyu da kuma wasu almajirai kafin dubunsu ta cika.
Sarkin na Zazzau ya bukaci al’umma da su ci gaba da jajircewa a duk lokacin da irin hakan ta taso.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaro da ’yan sintiri bisa namijin kokarin da suka yi na tabbatar da tsaro da kare kai.