✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Mabiya Darikar Kadiriyya sun gudanar da addu’o’i na musamman

Sheikh Karibullah ya yi kira da a ci gaba da yin addu'o'in sannan ’yan Najeriya tuba ga Allah su bar aikata sabo

Mabiya Darikar Kadiriyya a Najeriya sun gudanar da addu’o’i na musamman domin neman dauki daga Allah Ya kawo karshen mastalar tsaro da ta addabi kasar, musamman a yankin Arewa.

Da yake jagorantar taron addu’o’in, Shugaban Darikar Kadiriyya na Afirka ta Yama, Sheikh Muhammad Karibullah Nasiru Kabara, ya ce gudanar da irin addu’o’in a duk lokacin da wani bala’i ya samu mutane, koyarwa ce ta Annabi Muhammad (SAW).

“Idan muka yawaita addu’o’i, Allah zai amsa rokonmu kuma in Allah Ya yarda Allah zai fitar da mu daga wannan hali da muke ciki,” saboda haka yin shi abu ne mai muhimmanci idan aka shiga cikin tsanani, inji malamain.

Shugaban na Kadiriyya ya kuma bayyana cewa gudanar da addu’ar ta zama dole duba da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya da sauran sassan duniya, wanda abin damuwa ne.

Sheikh Karibullah ya yi kira ga daukacin ’yan Najeriya da su dage da rokon Allah Ya kawo karshen matsalar tsaro, sannan su tuba ga Allah su daina aikata sabo.

Ya yi kira da a ci gaba da yin addu’o’in a kullum tare kulla kyakkyawar mu’amala da nuna kyawawan dabi’u a tsakanin mutane da kuma tsakaninsu da Mahaliccinsu.

“Mu koma mu duba yadda tsakaninmu yake da Mahaliccinmu, mu tuba, mu daina aikata sabo, mu rika taimakon marasa shi tare da yin biyayya ga mahaifa,” inji malamin.

Shugaban na Kadiriyya ya kara da cewa ana bukatar mata da kananan yara da tsofaffi su rika halartar irin wadannan taruka, saboda haka ya bukaci a isar da sakon ga wadanda ba su samu halartar na ranar Lahadin ba.

Sheikh Karibullah ya shawarci Musulmi da su yawaita yin Salati ga Annabi Muhammad (SAW) da yin Istigfari da karatun Alkur’ani a kowace rana, sannan su yawaita addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.