Gwamnatin jihar Yobe ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana na jihar dake Kananan Hukumomi 17 har sai abin da hali ya yi.
Ko da yake jihar ba ta bayar da cikakken bayani kan makasudin daukar matakin ba, Aminiya ta gano cewa hakan ba zai rasa nasaba da satar daliban da aka fuskanta a jihohin Katsina da Neja da Zamfara a ’yan kwanakin nan ba.
- An sako daliban Makarantar GGSS Jangebe
- ’Yan bindiga sun sake kai hari wata makaranta a Kagara, sun sace mutum bakwai
Wata majiya a daya daga cikin irin wadannan makarantun wanda bai amince a ambaci sunansa ba ya ce an yanke hukuncin daukar matakin ne a karshen wata tattaunawa da mahukuntan jihar suka yi da sanyin safiyar ranar Lahadi.
A cewar majiyar, tuni iyayen yara da taimakon wasu jami’an tsaro suka je Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati dake Damaturu domin kwashe yaransu zuwa gida.
Sai dai sanarwar ta ce umarnin bai shafi daliban aji uku na manyan makarantun sakandire ba.
Sai dai yunkurinmu na jin ta bakin Kwamishinan Ilimi na jihar, Dokta Sani Idris ya ci tura saboda ance ba ya ofis ranar Lahadi kuma bai amsa kiran da aka yi masa ko dawo da amsa ga rubutaccen sakon da aka tura masa bay a zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya dai na dada daukar sabon salo kusan a kowacce rana inda a yanzu ’yan bindiga suka koma satar daliban makarantun kwana.
Ko a ranar Juma’a dai said a ’yan bindiga suka sace sama da dalibai ’yan mata 300 a wata makarantar sakandire a garin Jangebe a jihar Zamfara, kusan mako daya kenan da sace wasu 42 a wata makarantar dake Kaga a jihar Neja.