Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana aniyarsa ta aiki kafada da kafada da mafarauta don kawo karshen matsalar tsaro a Jihar.
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakoncin Kungiyar Mafarauta ta Najeriya a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lafia a ranar Alhamis.
- Dole ce ta sa makiyaya suka fara amfani da AK-47 – Gwamnan Bauchi
- Ya kamata a hana makiyayan kasashen waje shigowa Najeriya kiwo – Ganduje
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu
“Abin da nake so shi ne ganin yadda gwamnati za ta yi aiki tare da su sannan a bunkasa rayuwarsu.
“Abu ne mai kyau yin aiki tare da su saboda yadda suke taimakon rayuwar mutane suna kuma da daraja a idonmu sosai,” a cewar gwamnan.
Ya ce gwamnatinsa za ta tallafa wa mafarauta ta hanyar da za su taimaki jihar wajen yakar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Sannan ya ja hankalin kungiyar ka hada kan ’ya’yanta don samun tagomashi da cigaba a rayuwar yau da kullum.
Da yake nasa jawabi, Babban Kwamandan Kungiyar, Joshua Shateme, ya ce ya ji dadin yadda Gwamnatin Jihar ta dauke su da muhimmanci.
Shateme ya bayyana kudirinsu na yin aiki tare da Gwamnatin Jihar wajen yakar bata gari a jihar.
Sannan ya jinjina wa gwamnan kan yadda yake kokarin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa ta Tsakiya.