Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince ya bayyana gaban majalisar don yi wa ‘yan Najeriya bayani game da matsalar tsaro.
Gbajabiamila ya bayyana hakan ne ga ‘yan jarida a ranar Laraba, jim kadan bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar Villa dake Abuja.
- Boko Haram ta yi wa manoma 43 yankan rago a Borno
- Harin Zabarmari: Buhari ya jajanta kan kisan manoma 43
- Yadda ’yan Najeriya suka fusata da kisan manoma a Borno
- Kisan Zabarmari: Majalisa ta shawarci Buhari a kan Hafsoshin Tsaro
Kakakin ya ce Buhari zai bayyana gaban majalisar ne domin yi wa ‘yan Najeriya cikakken bayani game da matsalar tsaro da take kara tabarbarewa a kullum.
Sai dai bai bayyana ranar da Buhari zai bayyana gaban majalisar ba, inda yace sai nan gaba kadan za a sanar da ranar ga ‘yan kasa.
Ya kara da cewa ‘yan majalisar sun koka game da halin da kasar ke ciki, wanda hakan ne yasa ya amince ya bayyana gaban majalisar domin yi mata bayani.
Kakakin majalisar ya ce Buhari shugaba ne dake martaba dimokuradiyya saboda amincewarsa da gayyatar.
Gbajabiamila ya ce Buhari ya damu matuka da halin da kasar nan ke ciki na matsalar tsaro.