Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da wasu cikin gwamnonin Arewa da kuma shugabannin hukumomin tsaro domin nemo mafita mai dorewa ga matsalar tsaro a yankin.
Taron da aka gudanar a zauren Majalisar Zartaswa ta Tarayya da ke Fadar Shugaban Kasa an yi shi ne a wani mataki na magance kalubalen tsaro da ya addabi wasu yankunan Arewa.
Wata majiya daga Fadar Shugaban Kasa ta ce “Batun nemo mafita mai dorewa kan matsalar tsaro a jihohin Arewan da suka halarci zaman aka tattauna; matsalolin da duk jihohin da ake wakilta suke fuskanta kusan iri daya ne — ’yan bindiga da kuma ta’addanci.
“Don haka taron ya kasance kamar wata mahada ce da za a zauna don tattauna mafita,” in ji majiyar.
Wadanda suka halarci taron a ranar Juma’a sun hada da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong da takwaransa na Jihar Borno, Babagana Zulum da Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da takwaransa na Jihar Neja, Abubakar Sani Bello.
Sauran su ne Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da kuma Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkawato tare da Gwamnan Jihar Kebi, Atiku Babugu.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano da na Jigawa, Abubakar Badaru, suna cikin mahalarta taron, amma gwamnonin Katsina da Yobe, wato Aminu Bello Masari da Mai Mala Buni, ba su halarci zaman ba.
Taron ya kuma samu halartar Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (murabsu); Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (murabus); Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor; Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Bais Admiral Awwal Gambo; da kuma Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Isiaka Oladayo Amao.
Ragowar sun hada da Babban Sufeton ’Yan Sanda, Usaman Alkali Baba Usman; Darakta-Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya, Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Tara Bayanan Sirri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.