✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Aisha Buhari ta tayar da kura

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta jawo ce-ce-ku-ce bayan ta kaddamar da wani #maudu’in adawa da matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya. A ranar Lahadi…

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta jawo ce-ce-ku-ce bayan ta kaddamar da wani #maudu’in adawa da matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

A ranar Lahadi Aisha Buhari ta wallafa maudu’in mai taken #ArewaMufarka a  sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Sakon data wallafa ya hada da wani bidiyo da kuma hotunan wasu mutane dauke da kwalayen maudu’an zanga-zangar neman ama matsalar tsaro a Najeriya masu taken #EndInsecuritynow, #EndBanditryNow da kuma #AllLivesmatter.

An kalli bidiyon da ta wallafa akalla sama da sau 360,000.

Ko a ranar Asabar Aisha Buhari ta wallafa wani sako dauke hoton Shugaba Buhari da Hanyan Hafsoshin Tsaron Kasa wanda da a ciki ta sanya maudu’in #AceciJama’a.

Matakin nata ya haifar da muhawara inda wasu masu sharhi a kan sakon nata ke ta yaba mata a matsayin wacce ta damu da jama’a wasu kuma na kushe ta da cewa tana kware mijinta baya.

“Kimar uwarmu Aisha Buhari ta karu a wurina. Ba na tantamar yadda take kaunar talakawa.

“Ko a baya ta sha tsage gaskiya kan gazawar wannan gwamnatin da kurakurai a Fadar Shugaban Kasa.

“Ina amfani da wannan dama in bayyana goyon bayana gare ta saboda hikimarta da jajrcewarta da kuma yadda take nuna kulawa ga talakawa”, inji Victor Okezie, a sharhinsa ga sakon nata.

Mohammed Ajiya ya ce “Abun takaici, shin kina nufin yanzu ba ki da muhimmanci ne matsayinki na Matar Shuganan Kasa kuma Aminiya, har za ki zo sshafukan zumunta kafin a sauraren ki?”

Shi kuma Mohammed Bello ya ce, “Ya yi kyau, Matar Shugaban Kasa, mun gode.

“Don Allah ki isar da irin wannan sako ga mijinki, Shugaba Muhammadu Buhari”.

Obembe Aderogbayimi, ya ce, “Ina matukar ganin girman matar nan. Hakika kin isar da muhimmin sako”.

“Haka ya yi… Ina fata za su hada karfi su magance matsalar ‘yan bindiga a Arewa”, inji Umar Isyaku Yaro.

Usman Abubakar ya ce, “Ba na nadamar zabar Shugaba Buhari kuma na tabbata mutumin kirki ne da ke nufin Najeriya da alheri.

“Wasunmu sun kosa ne kawai su ga canjin da suka zaba.

“Allah Ya ba shi ikon yi da kyau”.

Shi kuma Abdul Alfa cewa ya yi, “‘Yan Najeriya masu fatar alheri na lura da ke.

“Kin isar babban sako ga masu ji da kuma hangen nesa, kukan kurciya jawabi ne”.

“Muna yabawa Matar Shugaban Kasa.

“Muna fata za ki dage da kokari domin ganin Shugaban Kasa na kallon abubuwa daga mahanagar talakawa ba ‘yan fada da ke zagaye da gwamnatinsa ba, da ke nesanta shi da talakawan da ke tare da shi tun kafinn ya hau mulki”, inji wani sakon

Idan ba a manta ba tun a makon jiya, a Arewacin Najeriya aka fara gudanar da zanga-zanga game matsalar wadda ta fi kamari a yankin.

Arewacin Najeriya na fama da matsalolin tsaro da suka hada da rikicin Boko Haram, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, rikicin manoma da makiyaya da kuma na kabilanci.

Zanga-zangar wadda tun da farko gamayyar kungiyoyin Arewa ta CNG ta kira, na neman gwamnati ta kawo karshen matsalolin tsaro a matsayin babban jigonta, duk da cewa ta yi kira da a bude jami’o’i sannan dole gwamnati ta soke yarjejeniyar kara farashin wutar lantarki da na man fetur.

Ta biyo bayan amsawa tare da alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na biyan bukatun masu zanga-zangar neman rushe rundunar ‘yan sanda na SARS da kuma kawo karshen kama karyar da jami’an ‘yan sanda ke yi wa jama’a.