Hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano na cacar baki da kamfanin wutar lantarki a jihar Kano (KEDCO) kan rashin ruwan famfo da ya addabi birnin Kano.
Hukumar na zargin kamfanin da kin samar da isasshiyar wuta a tsashoshin ruwa an Tamburawa da Challawa, lamarin da ke hana tayar da injinan ruwa, duk da makudan kudaden da take biyan KEDCO a duk wata.
“Gwamnatin jiha na kashe wa hukumar Naira miliyan 500 a wata, muna biyan KEDCO Naira miliyan 150 domin ta ba mu wuta na awa takwas a kullum, amma ba mu samun wutar yadda ya kamata musamman a matatar ruwa ta Tamburawa”, inji shugaban kamfanin Garba Ahmed Bichi.
Ya ce rashin samun wuta a matatar ta Tamburawa da ke samar da ruwan sha ga kananan hukumomi takwas da ke kwaryar birnin Kano shi ne musabbabin matsalar ruwar.
Maganar gwamnati sokiburutus ne
Sai dai a martaninsa, KEDCO ya yi fatali da zargin hukumar a matsayin mara tushe da kuma neman dora wa wani laifi.
Kakakin kamfanin Ibrahim Sani Shawai, ya ce “an samu karuwar wutar lantarki a dukkannin yankunan da ke karkashin KEDCO a watanni uku da suka gabata kuma jama’ar birnin Kano shaidu ne.
Sanarwar da ya fitar ta ce layukan wuta na Tamburawa da Challawa muhimmai ne ga KEDCO kuma “suna samun wuta a koyaushe matukar da wuta a Najeriya; don haka zargin da zargin da hukumar ke yi ba shi da tushe a wurinmu”.
Ibrahim Shawai ya kalubalanci hukumar da ta amsa gazawarta wajen sauke nauyin da ke kanta na samar da ruwan sha ga mazauna birnin Kano, wadanda don dole suka koma dogaro da ’yan garuwa ba tare da lura da wurin da suke samo ruwan ba.