Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa matsalar rashin zuwan yara mata makarantu ta fi tsananta a Arewacin Najeriya.
UNICEF ya bayyana hakan ne yayin da ya kuma tabbatar da alkaluman cewa fiye da kashi 50 na yara mata a kasar ne ba sa zuwa makaranta.
- Kotu ta tabbatar wa APC nasarar zaben gwamnan Benuwe
- Ba wanda zai karbi mulki daga Buhari ya tabuka wani abu a kwana 100 —Shehu Gabam
Da ya ke jawabi gaban taron inganta ilimi da makarantun Faransa a Najeriya suka shirya, Jutaro Sakamoto, shugaban sashen ilimi na UNICEF ya ce yanzu haka akwai akalla yara mata miliyan 7 da dubu 600 wadanda ba sa zuwa makaranta a sassan kasar.
A cewar jami’in na UNICEF, wannan adadi ya kunshi yara mata miliyan 3 da dubu 900 da ya kamata a ce suna matakin firamare baya ga wasu miliyan 3 da 700 a matakin karamar Sakandire.
Sakamoto ya bayyana cewa, kashi 48 na adadin yaran mata da ba sa zuwa makaranta na yankin Arewa maso Yammaci da Arewa maso Gabashin Najeriyar ne, yayin da matsalar nuna fifiko wajen karatun yara maza da takwarorinsu mata ke ci gaba da ta’azzara musamman a jihohin Arewacin 15.
Cikin makalar da jami’in na UNICEF ya gabatar, ya bayyana cewa kashi 9 ne kadai na yara mata da suka fito daga gidajen talakawa ke iya karatu a makarantun sakandire.
Kafin yanzu dai, Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda ake ci gaba da samun yara mata da ba sa samun damar zuwa makarantu a sassan Najeriya.
MDD ta nannata cewa wannan matsalar na ci gaba da ta’azzara ne sakamakon tsananin talauci da al’umma ke fama da shi baya ga matsalolin tsaro da suka yi wa wasu jihohin Najeriya katutu sai kuma nuna fifiko wajen bai wa yara maza ilimi fiye da mata da iyaye ke ci gaba da yi.