Salam edita, don Allah kabani dama in mika kokena ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur. Hakika man fetur wani muhimmin abu ne da ya ta’allaka ga rayuwar al’umma kai tsaye, idan ya wadata to al’umma zasu wadata musamman da abubuwan more rayuwa, haka zalika idan ya yi karanci to al’umma za su shiga cikin mawuyacin halin tsadar rayuwa. Matsalar karancin man fetur a Najeriya na neman tafi karfin mahukuntan kasar, dalilin cewa haka kuwa shi ne; tsawon lokacin da aka kwashe ana matsalar karancin man fetur da takai kusan watanni biyar koma fiye da haka ba tare da an shawo kan matsalar ba.
Babban abin mamaki, shi ne, babu wanda zai fada maka ga hakikanin dalilin da ya sa matsalar taki ci taki cinyewa, tun daga gwamnati zuwa dillalan man fetur din ko masu gidajen man, balle wasu daga cin al’umma da ke taimakawa domin wannan matsalar ta dore su kuma su yi ta amfana.
Idan na dauki bangaren gwamnati a farko za mu ga cewa, ita ce ke da hakkin kulawa da kowa da komai, kuma ita ke da ikon hakko man, tare da saida shi ga masu ikon saye, sannan ta yi tanadin ka’idoji da dokokin yadda za a yi saye da sayar da shi a gidajen mai, sannan ita ce ke da doka da oda a hannunta, tare da ikon hukunta duk wanda ya karya dokar da ta saba wa tsarin saye da sayar da man. Amman abin tambaya ga mahukuntan Najeriya shi ne; adaidai wannan lokacin da farashin gangar danyen man fetur ta fadi a kasuwannin duniya, kuma lokacin da ya kamata man fetur ya zama kamar ruwan sha a kasar sai ga shi ya yi wahalar da ba a taba gani ba a tarihin kasar., Ko me ya kawo haka? Wannan tambaya ce da ya kamata Gwamnatin Najeriya tare da masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur su yi wa al’ummar kasa bayani domin fayyace masu abin da yasa haka.
Idan na koma bangaren dillalan man fetur din wadanda su ne ke da hakkin saye daga gwamnati tare da sayar da shi ga al’ummar kasa a gidajen man za mu ga cewar suna alakanta wahalar man da cewa, ba su samunsa yadda ya kamata balle su ma su saida ko kuma suna ta’allaka lamarin da cewar ka’idojin da aka gindaya masu kafin sawo man sun yi tsauri. Don haka man ke karanci gare su. Amman mafi yawa daga cikin al’ummar gari ba su gamsu da hujjojin da dillalan man ke bayarwa ba. Domin suna zargin su da tsawwala wa al’umma tare da boye man a gidajen mansu. Wannan zargi dai sun kasa musantawa.
Tabbas ya zama wajibi mu sanar da Gwamnatin Tarayyar Najeriya da sauran dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren albarkatun man fetur su sani cewar; har yanzu ana fama da matsalar karancin man fetur a manyan biranan kasar, sannan har yanzu wasu gidajen man na sayar da shi akan farashin da ransu yake so, wanda ya kai har sama da naira 150 a farashin kowace lita, maimakon naira 86.5 kamar yadda doka ta tanada a yanzu, sanadiyyar haka kuwa tasa ana dogayen layi a gidajen man mallakar Gwamnati da na ‘’yan kasuwa masu sayarwa akan ka’ida.
Ina kira ga mahukuntan kasar mu baki daya su tuna karancin man fetur ya haddasa wahalhalu a harkar sufuri da tsadar abubuwan masarufi ga talakawa. Don haka ya zama wajibi ga Gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a fanni albarkatun man fetur su lalubo hanyar magance wannan matsalar da ta dauki tsawon lokaci tana ci wa al’umma tuwo a kwarya. Ina mai kare bayanina a karshe da addu’ar Allah ya sa wannan ya kai inda ya dace amin.
Adamu Aliyu Amo, Katsina. Sakataren kungiyar Muryar Jama’a, reshen Jihar Katsina. 09097300909 [email protected]
Matsalar karancin man fetur ta addabi al’umma
Salam edita, don Allah kabani dama in mika kokena ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur. Hakika…